Wannan ne karon farko da haka ta faru tun bayan da kungiyar Taliban ta karbe iko da Afghanistan a watan Agustan 2021. Hoto: AP Archive      

Kimanin 'yan mata 80 aka sa wa guba a abinci a makarantun firamare biyu kuma an kwantar da su a asibiti a lardin Sar-e-Pul da ke arewacin Afghanistan, kamar yadda wani jami'in hukumar ilimi ya sanar.

Mohammad Rahmani, wanda yake jagorantar bangaren ilimi na lardin, ya bayyana a ranar Lahadi cewa kusan 'yan mata 'yan makaranta 80 aka sa wa gubar a lardin Sangcharak.

Ya ce dalibai 60 aka sa wa guba a makarantar Naswan-e-Kabod Aab da wasu 17 da su ma aka sa musu gubar a makarantar Naswan-e-Faizabad.

“Duka makarantun firamaren suna kusa da juna kuma an yi hakan ne daya bayan daya," in ji shi.

"Mun garzaya da daliban asibiti kuma dukkansu sun warke."

Ana ci gaba da bincike, sai dai sakamakon farko ya nuna cewa wani mai mugun nufi ne ya biya wani don ya aikata hakan, in ji Rahmani.

Bai yi karin haske ba kan yadda aka saka wa 'yan matan gubar ko kuma kan yadda suka yi jinya.

Kazalika Rahmani bai bayyana ainihin shekarunsa ba, sai dai ya ce suna tsakanin aji 1 zuwa 6.

Karuwar sanya guba

An haramta wa 'yan mata a Afghanistan ci gaba da karatu daga aji shida na firamare, kuma ba a bari su je jami'a, sannan an haramta wa mata aikin gwamnati da kuma shiga wuraren taruwar jama'a.

Wannan ne karo na farko da aka saka guba a abincin 'yan makaranta tun bayan da Kungiyar Taliban ta karbi mulkin kasar a watan Agustan shekarar 2021 kuma daga lokacin ne suka fara take hakkin mata da 'yan mata a Afghanistan.

Kodayake makwabciyar Afghanistan wato Iran ta fuskanci karuwar sanya guba a abinci yawancin a makarantar 'yan mata da aka samu a watan Nuwamba.

Dubban dalibai ne suka fada rashin lafiya bayan faruwar al'amarin. Sai dai ba a iya gano wanda yake hannu ba kan al'amarin, kodayake ana da tabbacin an yi amafani da sinadarai masu guba.

TRT World