An yanke wa wani tsohon sojan Amurka hukuncin daurin shekara 55 a gidan yari saboda laifin kashe wani dan gudun hijirar Afganistan tare da nuna kyama ga addininsa na Musulunci.
Bayan shari'ar kwanaki uku, an yanke wa Dustin Passarelli hukunci a Jihar Indiana da ke tsakiyar yammacin Amurka da laifin kisan Mustafa Ayoubi, mai shekara 32, tare da karin wasu lokuta a kai saboda amfani da makami.
A lokacin kisan, Ayoubi ba ya dauke da makami, a lamarin da ya faru a watan Fabrairun 2019 a yammacin birnin Indianapolis.
Wani bincike da aka gudanar ya yi nuni da cewa an harbi Ayoubi har sau takwas, sau bakwai a bayansa.
A ‘arangamar’ da aka yi tsakanin mutanen biyu a kan hanya, Passarrelli ya bi Ayoubi ta babbar hanya da ke zuwa rukunin gidajen bakin haure da ke yankin, inda ya furta kalaman kyama ga addinin Musulunci, gami da cewa “ka koma kasarku,” kafin ya bude wuta, a cewar shaidu.
Da yake kokarin kare kansa, Passarrelli ya yi ikirarin yana fama da rashin lafiya ta damuwa wacce a cewarsa ta kai shi ga harbin da ya yi.
Passarelli bai fuskanci wasu tuhume-tuhume na nuna kiyayya ko kyama ba, saboda ya aikata kisan ne a daidai lokacin da ‘yan majalisar dokokin Indiana ke muhawara kan sabon kudirin dokar laifuka kan nuna kiyayya.
Bayan wasu makonni ne aka zartar da kudurin ta zama doka, inda aka tsawaita zaman gidan yari ga duk wasu ayyuka da suka shafi ‘son zuciya.’
“Iyalan Ayoubi da daukacin al'ummar Musulmai da ke Hoosier (Indiana) sun matukar kaduwa da wannan mataki," a cewar mai gabatar da kara na gundumar Marion Ryan Mears a zantawar da kafafen yada labarai na cikin gida suka yi da shi.
Ya kara da cewa "Ba za mu iya kawar da wannan matsala farat daya ba, amma ofishin gabatar da kara zai ci gaba da aiki wajen kai rahoton duk wani mutum da nuna kyama ko kiyayya a cikin al'ummarmu."