Gwamnatin Taliban ta ce dole ne a dakatar da duk wasu ayyuka da kasar Sweden ke yi a Afghanistan, bayan kona Kur'ani da aka yi a wajen wani masallaci da ke babban birnin kasar Sweden, a watan jiya.
"Bayan wulakanta Alkur'ani mai tsarki da kuma ba da izini ga cin mutuncin addinin Musulunci, gwamnatin Musulunci ta Afghanistan ta bayar da umarnin dakatar da duk harkoki ko ayyuka da kasar Sweden ke yi a Afghanistan," a cewar sanarwar da kakakin gwamnatin Taliban, Zabiullah Mujahid ya fitar a ranar Talata.
A yanzu haka dai, babu wani ofishin jakadancin kasar Sweden da ke bude a Afghanistan, tun bayan da kungiyar Taliban ta karbi ragamar mulkin kasar a shekarar 2021.
Kona Alkur'ani
Wani dan gudun hijirar kasar Iraki a Sweden ne ya kona Alkur'ani mai tsarki a wajen wani masallaci da ke birnin Stockholm a watan da ya gabata, lamarin da ya janyo bacin rai tare da tunzura al’ummar Musulmai a fadin duniya.
Kungiyar Kwamitin Sweden ta Afganistan ba ta mayar da martani nan take ba, kan bukatar yin tsokaci kan wannan umarni na Taliban.
Zuwa yanzu gwamnatin Taliban ba ta bayar da wani cikakken bayani kan kungiyoyin da wannan mataki zai shafa ba.