Tuni dai lamarin ya daga hankula inda aka shiga aikin ceto ba ji ba gani a Tekun Bahar Rum. /Hoto: OTHERS

Ana fargaba daruruwan 'yan ci-rani sun mutu bayan wani da kwale-kwalen kamun kifi da suke ciki ya nutse a tekun kasar Girka, a kan hanyarsa zuwa Italiya daga Libiya.

Tuni dai lamarin ya daga hankula inda aka shiga aikin ceto ba ji ba gani a Tekun Bahar Rum.

Firaiministan rikon kwarya na kasar Girka Ioannis Sarmas ya ayyana makokin kwana uku, saboda afkuwar daya daga cikin bala'o'in 'yan ci-rani mafi girma da suka faru a yankin, inda a kalla mutum 79 suka mutu.

Ana tsammanin daruruwan mutane ne a cikin jirgin a lokacin da ya nutse a ranar Laraba, duk da cewa akwai bayanai masu cin karo da juna a kan ainihin yawan mutanen.

Wata kungiyar agaji ta Charity Alarm Phone, da ke aiki a yankin don ba da taimako kan irin wadannan abubuwa, tun da fari ta ce ta samu sakonnin tashin hankali daga mutanen da ke cikin jirgin ruwan, da ke cewa akwai kusan mutum 750 a cikinsa.

Wasu rahotannin kuma sun ce fiye da mutum 500 ne suke cikinsa.

Masu aikin ceto sun ceto fasinjoji 104 da suka hada da 'yan kasashen Masar da Syria da Pakistan da Afghanistan da kuma Falasdinu, sannan an gano gawarwaki 79.

Kazalika an ci gaba da aikin ceton a ranar Alhamis inda ake amfani da jiragen sama don gano mutane.

TRT World