An kawo wani dattijo da ke fama da matsalar zafi asibitin gwamnati da ke cike da cunkoso a Ballia, jihar Uttar Pradesh da ke Indiya.Hoto: (Rajesh Kumar Singh/AP)

Wani tsananin zafi da aka yi a jihohi biyu mafi yawan al’umma a Indiya ya haifar da katsewar wutar lantarki, tare da sanya cunkoson mutane marasa lafiya a asibitoci inda dakunan ajiye gawarwaki suka cika makil.

Lamarin da ya tilasta wa ma’aikata yin amfani da littattafai wajen yin fifita ga marasa lafiya da ke kwance, yayin da jami'ai ke bincike da kuma tattaro adadin wadanda suka mutu, da ya zuwa yanzu ya kai kusan 170.

A jihar Uttar Pradesh da ke arewacin kasar, mutane 119 ne suka mutu sakamakon cututtuka masu alaka da zafi a 'yan kwanakin da suka gabata, yayin da makwabciyarta Bihar ta bayar da rahoton mutuwar mutane 47, kamar yadda rahotanni da jami'an kiwon lafiya suka fitar a ranar Talata.

A hira da kamfanin dillancin labarai na Associate Press ya yi da Jitendra Kumar Yadav, wani direban babbar mota a garin Deoria mai nisan kilomita 110 daga Ballia, ya ce "Mutane da dama suna mutuwa saboda tsananin zafin da ake ciki, ba mu samu lokacin hutu ko na minti daya ba. A ranar Lahadin da ta gabata, na dauki gawarwaki 26.”

Wasu mazauna garin sun ce suna tsoron fita waje da safe bayan rana ta fito.

Jami’ai sun ce dakin ajiye gawarwakin asibitin gundumar Ballia da ke Uttar Pradesh ya cika bayan gawar mutane 54 da aka ajiye, wadanda dukkansu tsoffi ne da suka yi fama da rashin lafiya daban-daban, sai kuma yanayin zafin da ake ciki ya yi ajalisun. An bukaci wasu iyalai da su kwashe gawarwakin ‘yan uwansu zuwa gida.

A ranar Lahadin, ministan lafiya na jihar Brajesh Pathak, ya ce wata tawaga ta mutane biyu za ta binciki musabbabin yawan mace-macen da aka samu da kuma adadin mutane nawa ne mutuwarsu ke da alaka da zafi kai tsaye.

Ana fuskantar yanayi na zafi fiye da yadda aka saba a yankunan arewacin Indiya da tuni yanzu aka shiga lokutan zafi na watannin bazara.

A cewar Sashen Nazarin Yanayi na Indiya IMD, yanayin da ake ciki ya kai maki 43.5 a ma'aunin salshiyos (digiri 110 Fahrenheit).

Ana ayyana yanayin zafi a Indiya idan ma’aunin zafi ya kai akalla maki 4.5 C sama da yadda aka saba gani kenan, ko kuma idan zafin ya wuce maki 45 C (113 F).

"Mun yi ta yin gargadi a 'yan kwanakin da suka gabata game da yanayi zafi da za a shiga," a cewar Atul Kumar Singh, masanin kimiyya a IMD.

Duk da gargadin da aka yi ta yi, jami'an gwamnati ba su nemi jama'a da su yi shiri kan zafin ba har sai ranar Lahadi, lokacin da adadin wadanda suka mutu ya fara karuwa.

Rashin isassun kayan aiki

Katsewar wutar lantarki a fadin yankin, ta kara tsananta yanayin zafin da ake ciki, inda mutane ke fama da datsewar ruwan famfo da na'urorin sanyaya iska.

Babban Ministan Uttar Pradesh, Yogi Adityanath ya ce gwamnati na daukar matakan tabbatar da samar da wutar lantarki ba tare da an samu katsewa ba. Ya bukaci ‘yan kasar da su ba da hadin kai wajen amfani da wutar lantarki cikin adalci.

“Ya kamata duk wani kauye da birni su samu isasshiyar wutar lantarki a wannan yanayi na zafi. Idan an samu wasu kura-kurai, to a gaggauta magance su,” in ji shi a cikin wata sanarwa.

A asibitin gundumar Ballia, irin cikan da mutane suka yi, ya sa an yi tuni da lokacin bullar cutar korona inda iyalai da likitoci ke ta kai komo don ba da kulawa ta gaggawa ga marasa lafiya nasu neman taimako.

Hanyoyin shiga cikin asibitin ya cike da warin fitsari da dattin shara ga kuma bangon asibiti da ya baci da ganyen bishiyar betel.

Babu na'urorin sanyaya iska a dakunan da ke asibitin, sannan fanka da aka saka musu ba sa aiki yadda ya kamata saboda katsewar wutar lantarki.

A gefe guda kuma ma’aikata asibitin ne suka rika fifita marasa lafiya takardu tare da goge guminsu a wani yunkuri na kwantar musu da hankali.

Jami'ai sun ce ana samun wasu munanan yanayi a asibitocin da ke wasu manyan birane da ke kusa da su kamar Varanasi, kuma tuni aka tura karin likitoci da kayayyakin kiwon lafiya zuwa asibitin gundumar don shawo kan wannan yanayi da zafi ya haifar.

Masana yanayi sun ce guguwar zafi za ta ci gaba kuma Indiya na bukatar ta yi shiri mai kyau don tunkarar sakamakon da zai biyo baya.

Wani bincike da ‘World Weather Attribution’, wata kungiyar ilimi da ke nazari kan tushen tsananin zafi da ake samu, ta gano cewa tsananin zafi a cikin watan Afrilu da ya afku a wasu sassan Kudancin Asiya, ya kasance akalla har sau 30 sakamakon sauyin yanayi da aka ciki.

TRT World