Hukumomo sun kama mutum tara da ake zargi da hannun a wannan fashewa./Hoto:  Reuters

A kalla mutum 31 ne suka mutu bayan fashewar wani abu a wani gidan cin abinci a birnin Yinchuan da ke arewa maso yammacin China, a cewar kafar yada labaran kasar.

"Wani yoyon iskar gas ne ya jawo fashewar a kantin cin abincin da ake gashin nama," in ji kamfanin dillancin labaran na Xinhua.

Ya kara da cewa lamarin ya faru ne a ranar Laraba da yamma, kuma mutum bakwai sun jikkata inda a halin yanzu suke asibiti ana duba su.

'Yan sanda sun kama mutum tara, ciki har da mai gidan sayar da abincin.

"Kamar yadda doka ta tanada, jami'an tsaro sun kama mutum tara, ciki har da mai gidan gasa naman, da masu ruwa da tsaki da kuma ma'aikata... sannan an kwace kadarorinsu," a cewar gidan talbijin na CCTV, yana mai ambato wani kwamiti na jam'iyyar gurguzu.

Za mu kawo muku karin bayani bayani nan gaba.

AFP