Yanayin zafi ko sanyi na iskar da aka saba ji a duniya yana kamawa ne daga12C zuwa kasa da 17C a kowacce rana,  / Hoto: Reuters

Ranar Litinin din da ta gabata an yi zafin da ba ta taba yin irin sa ba a duniya, inda ya haura digiri 17 a ma’aunin selshiyos a karon farko, a cewar hukumar kula da yanayi ta Amurka.

Yanayin zafi ko iskar da aka saba ji a duniya ya kai 17.01a ma’aunin selshiyos kamar yadda Hukumar da ke kula da Tekuna da Yanayi ta Kasa a Amurka [NOAA] ta bayyana.

An dauki wannan yanayi ne ranar Talata kuma ya zarta yanayi mafi yawa da aka bayyana ranar 24 ga watan Yulin bara wanda ya kai digiri 16.92C a ma’aunin selshiyos, a cewar bayanan NOAA, wacce ta bi diddigin irin wadannan bayanai tun daga 1979.

Yanayin zafi ko sanyi na iskar da aka saba ji a duniya yana kamawa ne daga 12C zuwa kasa da 17C a kowacce rana a shekara, kuma ya kai 16.2C a farkon watan Yuli a 1979 da 2000.

Zafi zai ci gaba da karuwa

Yawancin lokuta yanayin na zafi yana ci gaba da karuwa har zuwa karshen watan Yuli ko farkon watan Agusta.

Ko a watan jiya, yanayin da aka saba ji a Turai ya kai wanda ba a taba fuskanta ba.

A shekara mai zuwa yanayin zafi zai ci gaba da fiye da yadda aka taba fuskanta a duniya yayin da za a fuskanci yanayin kadawar iska mai zafi na El Nino a Kogin Pacific.

AFP