Yakin da ake yi a Sudan na kara yawan mutane da suka rasa matsuguninsu/ Hoto: Reuters

Sama da mutane miliyan 110 ne a duniya aka tilasta wa barin gidajensu, a cewar Majalisar Dinkin Duniya a ranar Laraba, inda ta bayyana wannan lamari na tashin hankali a matsayin "barazana" ga duniya.

Yakin da Rasha ke yi da Ukraine, da 'yan gudun hijirar da suka tsere daga Afganistan, da kuma fadan da ake ci gaba da gwabzawa a Sudan, sun sanya adadin 'yan gudun hijirar da aka tilasta wa neman mafaka fita zuwa wasu kasashe.

Kazalika adadin wadanda suka rasa muhallansu a kasashensu ya kai matakin da ba a taba gani ba, a cewar hukumar kula da 'yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya UNHCR.

A karshen bara, mutane miliyan 108.4 ne suka rasa matsugunansu, a cewar rahoton UNHCR mai taken Global Trends in Forced Displaced wada ta saba fitarwa a duk shekara.

Adadin ya haura miliyan 19.1 a karshen 2021- kari mafi yawa tun daga lokacin da aka fara tattara sakamokon a shekarar 1975.

Tun daga lokacin, rikici a Sudan ya barke inda ya kara yawan mutanen da suka rasa mutsugunansu a duniya, adadin da ya kai miliyan 110 a watan Mayu.

"Muna da mutane miliyan 110 da suka yi gudun hijira saboda tashe-tashen hankula da tsanantawa da kuma nuna musu wariya da cin zarafinsu da tasirin sauyin yanayi," in ji shugaban hukumar UNHCR Filippo Grandi a wani taron manema labarai da aka yi Geneva.

"Wannan yanayi abin tsoro da takaici ne ga halin da duniyarmu ke ciki," in ji shi .

Rahoton da hukumar UNCHR ta fitar ya nuna cewa adadin ya hada mutanen da suka rasa matsuguninsu miliyan 62.5 da ‘yan gudun hijira miliyan 35.3 da masu neman mafaka miliyan 5.4 da kuma mutane miliyan 5.2 da ke bukatar kariya.

Yara

Mafi yawan nauyin dai na kan kasashe masu karamin karfi da matsakaita, yayin da suke karbar bakuncin kusan kashi 76 cikin 100 na 'yan gudun hijirar duniya da sauran mutanen da ke bukatar kariyar kasa da kasa.

Rahoton ya ce kasashe da ke da mafi karancin ci gaba sun ba da mafaka ga kashi 20 cikin 100 na jimillar masu neman mafaka, yayin da kashi 70 cikin 100 na kasashen da ke makwabtaka da kasashensu na asali suka ba su mafaka.

Rahoton ya jaddada cewa Turkiyya ce ke da mafi yawan 'yan gudun hijira a duniya da adadin kusan 'yan gudun hijira miliyan 3.6.

Sai Iran da ke biye mata da miliyan 3.4, yayin da Colombia ke da adadi miliyan 2.5 sai kuma Jamus mai miliyan 2.1.

A halin da ake ciki, yara da ke da kashi 30 cikin 100 na yawan al'ummar duniya, sun wakilci kashi 40 cikin 100 na jimillar mutanen da aka tilasta musu yin hijira, a cewar rahoton.

Har wa yau rahoton ya ce Amurka ce kasa ta farko da ta fi karbar mutane a duniya, yayin da ta samu mutane da suka nemi mafaka 730,400 daga cikin jimillar mutane miliyan 2.6 a shekarar 2022.

UNHCR ta ce ana bukatar kara kaimi don taimakawa 'yan gudun hijira. Hoto: Reuters

Sai kuma kasar Jamus da ke bin bayan Amurka da adadi 217,800 sai kuma kasar Costa Rica da Sifaniya da kuma Mexico da suka hade kasashe biyar da ke kan gaba.

Jinkiri wajen samun mafita

Rahoton ya jaddada cewa kashi 52 cikin 100 na jimillar 'yan gudun hijira da sauran mutanen da ke bukatar kariya ta kasa da kasa sun fito ne daga kasashe uku da suka hada da: Syria (miliyan 6.5) da Ukraine (miliyan 5.7) da kuma Afghanistan (miliyan 5.7).

Adadin 'yan gudun hijira a duniya baki daya ya karu da kashi 35 cikin 100, wato mutane miliyan 8.9 kenan, sannan zuwa miliyan 34.6 a karshen shekarar 2022, a cewar rahoton.

Kazalika rahoton ya bayyana cewa karin da aka samu ya bayan ‘yan gudun hijira daga Ukraine da suka tsere daga yakin da ake yi a kasarsu da kuma adadin da kiyasta na ‘yan Afghanistan a Iran da Pakistan.

“Wadannan alkaluman sun nuna mana cewa wasu mutane na saurin shiga rikici sannan suna wuyar samun mafita,” in ji Filippo Grandi, kwamishinan kula da ‘yan gudun hijira na Majalisar Dinkin Duniya.

“Sakamakon hakan na ta da hankula, tare da sanya mutane kaura daga matsuguninsu da kuma sanya miliyoyin mutane da aka tilasta musu barin matsugunansu cikin yanayi na bakin ciki.”

MDD ta ce adadin mutanen da su ka rasa mastuguninsu na iya karuwa/ Hoto: Reuters

Rahoton ya kuma nuna wasu ci gaba da aka samu inda mutane miliyan shida da suka rasa matsugunansu suka koma kasashensu na asali a shekarar 2022, wadanda suka hada da mutanen 5.7 da suka rasa matsuguninsu da kuma ‘yan gudun hijira 339,300.

Haka kuma, an sake tsugunar da 'yan gudun hijira 114,300, adadin da ya ninka na shekarar da ta gabata da (57,500) a cewar kididdigar gwamnati.

Sannan hukumar ta UNHCR ta mika 'yan gudun hijira 116,500 zuwa jihohinsu don sake tsugunar da su, kamar yadda rahoton ya bayyana.

"Yayin da adadin mutane da aka tilaswa barin matsuguninsu da 'yan gudun hijirar da suka samu mafaka ya karu a shekarar 2022 idan aka kwatanta da shekarar da ta gabata, samun mafita wacce za ta dore na ci gaba da haifar da fargaba ga sauran," in ji rahoton.

A 2022, akalla 'yan gudun hijira miliyan 5.7 suka koma wurarensu na asali, fiye da kashi 8 cikin 100 na idan aka kwatanta da shekarar da ta gabata, a cewar rahoton.

Rahoton ya kara da cewa daga cikin kowane dan gudun hijirar da ya dawo ko aka sake tsugunar da shi a shekarar 2022, akwai sabbin ‘yan gudun hijira 16.

TRT World