An gudanar da gagarumin gangami a kasar ta Koriya ta Arewa ranar Lahadi domin tunawa da Yakin Koriya wanda kasar ta balle shekaru 73 da suka gabata, / Hoto: AP

Koriya ta Arewa ta gudanar da gagarumin gangami a babban birnin kasar Pyongyang inda mutane suka rika ihu suna shan alwashin yin "yakin ramuwar gayya" do kawar da Amurka.

Sun yi gangamin ne a yayin bikin kasar na ballewa don kafa kasarsu bayan yakin Koriya shekaru 73 da suka gabata.

Ma'aikata da dalibai kusan 120,000 ne suka halarci gangamin a fadin babban binrin kasar ranar Lahadi, kamar yadda kamfanin dillancin labaran kasar KCNA ya rawaito a yau Litinin.

Hotunan da kamfanin dillancin labaran ya wallafa sun nuna dandazon mutane sun cika filin wasa dauke da kwalayen da aka rubuta "Amurka baki dayanta ba ta yi mana nisa don harbe ta ba" da kuma "Amurka mai mulkin mallaka tana kawar da zaman lafiya."

An yi bikin na ranar Lahadi ne a yayin da ake ci gaba da nuna fargabar cewa Pyongyang za ta iya harba wani sabon tauraron dan adam dinta na soji da ke iya yin leken asiri kan ayyukan da sojojin Amurka bayan yunkurin da ta yi na harba shi ranar 31 ga watan Mayu bai yi nasara ba.

'Amurka mai mulkin mallaka'

Yanzu Koriya ta Arewa tana da "makamai mafi karfi domin hukunta Amurka mai mulkin mallaka" kuma "masu son yi ramuwa na kasar nan sun matsu su dauki fansa kan makiya," in ji KCNA.

Koriya ta Arewa ta dade tana gwaji makamai daban-daban ciki har da babban makaminta mai linzami da ke tafiyar dogon zango, lamarin da ya sa ake zaman dar-dar a Koriya ta Kudu da babbar kawarta, Amurka.

A wani rahoto na daban da ma'aikatar wajen kasar ta fitar, Koriya ta Arewa ta ce Amurka "tana yin fadi-tashin ganin ta farfado da yakin makaman nukiliya," inda ta zargi Washington da laifin tura wasu bayanai na musamman yankin.

TRT Afrika da abokan hulda