Mafi yawan asarar dukiya da aka samu a tsakanin 1970 da 2021 sun afku a Amurka, wanda ya kai yawan dala tiriliyan 1.7/ Hoto: TRT World

Asarar da dumamar yanayi da ibtila’o’in da sauyin yanayi ke janyowa na kara daduwa, duk da cewar gargadi da wuri na taimaka wa wajen rage radadin matsalolin, in ji Hukumar Hasashe da Yanayi ta Majalisar DInkin Duniya (WMO).

Hukumar Hasashe da Kula da Yanayi ta Majalisar Dinkin Duniya (WMO), a wani sabon rahoto da ta fitar a ranar Litinin din nan ta bayyana cewa an samu kusan afkuwar ibtila’o’i na yanayi da ambaliyar ruwa kusan 12,000 a rabin karnin da ya gabata, inda sama da mutum miliyan biyu suka rasa rayukansu, aka kuma yi asarar da ta kai dala tiriliyan 4.3.

Wannan rahoto daga hukumar na zuwa ne a lokacin da ta fara gudanar da taron da ta saba yi duk bayan shekara hudu tsakanin mambobinta, inda ta bayyana cewa ana bukatar zage damtse sosai don cimma manufar yaki da matsalolin, nan da 2027.

Hukumar ta bayyana cewa za a ci gaba da samun asarar dukiya sakamakon ibtila’o’in da munanar yanyi da ambaliyar ruwa ke janyowa.

Hukumar ta ce “Asarar dukiya da kadarori na daduwa. Amma kuma gargadi da wuri da shirya tunkarar ibtila’i a kan lokaci na rage asarar da dan adam ya fuskanta a shekara 50 din da suka gabata.”

Hukumar da ke birnin Geneva, ta sha yin gargadi game da tasirin da ake fuskanta sakamakon gurbatar yanayi da dan adam ke yi, inda ta ce ana samun karuwar zafi, sannan ambaliyar ruwa da guguwa da tsananin zafi da fari na kara yawaita.

Hukumar ta kuma ce tsarin bayar da gargadi da wuri ya taimaka sosai wajen rage adadin wadanda suke mutuwa sakamakon rikice-rikicen da suke da alaka da munanar yanayi.

Mafi yawan asarar dukiya da aka samu a tsakanin 1970 da 2021 sun afku a Amurka, wanda ya kai yawan dala tiriliyan 1.7.

Tasiri kan tattalin arzikin ya fi illa a kasashe masu tasowa, idan aka yi duba da arzikin da kasashen ke samu.

Gargadi da wuri na kubutar da rayuka

Sakatare Janar na Hukumar Hasashe da Kula da Yanayi ta MDD, Petteri Taalas ya sanar da cewa mummunar guguwar Mocha da ta afku a Myammar da Bangaladash a wannan watan ta zama misalin “yadda al’ummu da ba su da katabus suke shan wahalar munanar yanayi, da ibtila’o’in da ke da alaka da ruwa da sauyin yanayi.”

Ya ce “A baya, Myammar da Bagaladash sun fuskanci mutuwar dubban mutane,” inda yake bayar da misali kan gargadi a kan lokaci da cewa “Madalla ga gargadi da wuri, a yanzu yawaitar mace-mace sakamakon ibtila’o’i ya ragu sosai.”

Ya ce, “Gargadi da wuri na kubutar da rayuka.”

An fitar da sakamakon bincike kan shekaru 50 da suka gabata, inda aka duba asarar dukiya da kadarori da aka yi a duniya sakamakon munanar yanayi da ibtila’o’in da ambaliyar ruwa ke janyowa.

Hukumar ta kuma tabo wasu gargade-gargade game da rahoton nata: A lokacin da ibtila’o’in suka karu sosai, akwai yiwuwar an tsallake wasu saboda karin da aka samu a bangaren rahotannin da suka shafi tsananin illar munanar yanayi.

A duk duniya, guguwa a yankunan da ke da zafi ne suka fi janyo asarar rayuka da dukiyoyi ga jama’a.

A Afirka, Hukumar ta kirga sama da ibtila’i 1,800 da rasa rayuka 733,585 da munanar yanayi ya janyo, illolin da ambaliyar ruwa da sauyin yanayi suka janyo da suka hada da guguwa. Mafi muni ita ce guguwar Idai a 2019 wadda ta janyo asarar dala biliyan 2.1.

Kusan ibtila’i 1,500 ne suka afku a kudu maso-yammacin Tekun Pacific, inda suka janyo asarar rayuka 66,951 da dukiya da ta kai darajar dala biliyan 185.8.

Asiya ta fuskanci ibtila’i 3,600 da suka sun janyo asarar rayuka 984,263 da kuma dala biliyan 1.4. Kudancin Amurka kuma ya fuskanci ibtila’i 943 da asarar rayuka 58,484 da kuma sama da dala biliyan 115.

Sama da ibtila’i 2,100 ne suka afku a Arewacin Amurka da Tsakiyar Amurka da Karibiyan wadanda suka janyo mutuwar mutum 77,454 da asarar dala tiriliyan biyu.

Turai kuma sun fuskanci kusan ibtila’i 1,800 wadanda suka yi ajalin mutum 166,492 da janyo asarar dala biliyan 562.

A makon da ya gabata hukumar ta yi hasashe da kashi 66 kan cewar nan da shekaru biyar masu zuwa, duniya za ta dumama da karin daraja 1.5 a ma’aunin salshiyos, wanda ya haura dumamar da aka samu a tsakiyar karni na 19, inda zai kai matakin da taron sauyin yanayi na Paris na 2015 ya yi hasashe.

TRT World