Mutane sun cika a filin tashi da saukar jiragen sama na Frankfurt lamarin da ya sa aka soke ko jinkirta da tashin wasu jirage saboda guguwar ambaliya / Hoto: Reuters

Ruwan sama kamar da bakin kwarya ya jefa filin jirgin sama mafi girma na Frankfurt a Jamus cikin rudani, lamarin da ya haifar da soke tashi da saukar jiragen sama kusan 100 da kuma jinkirta tashin wasu da dama.

Ruwan sama ya mamaye titin jirgin da yammacin ranar Laraba, inda daruruwan fasinjoji suka makale a cikin jiragen na tsawon wasu sa'o'i.

Guguwar ta sanya saukar ruwa mai yawan gaske tare da walkiya na kusan sa’a guda.

Wasu jerin bidiyoyi da aka yada a shafukan sada zumunta sun nuna yadda ruwa ya rufe manyan titunan jiragen saman.

An dakatar da duk wasu ayyukan kasa na filin jirgin saman har na tsawon awanni biyu, an soke saukar sama da jirage 20 da suka nufi Frankfurt zuwa wasu filayen jiragen sama.

A sanarwa da sashen da ke kula da tashar filin jirgin saman ya fitar, ya ce yanayin zai shafi jadawalin lokutan tashin jirage na ranar Alhamis sannan akwai yiwuwar samun karin sokewa ko jinkirin wasu jiragen.

“Ya kamata fasinjoji su duba lokutan tashi daga kamfanonin jiragensu. Saboda karuwar yawan fasinja, muna ba dukkan fasinjoji shawara da su isa filin jirgin sama sa'o'i biyu da rabi kafin lokacin tashin jirginsu," a cewar sanarwar.

Ambaliyar ruwan ta mamaye gine-gine sama da 350 tare da kayar da bishiyoyi sama da 17, kazalika an gayyaci wasu jami’ai da ba sa aiki domin su taimaka.

Guguwar ta kuma shafi wasu yankuna, kamar Gelsenkirchen da kuma yankin North Rhine-Westphalia inda lamarin ya yi kamari.

Kan tituna da wuraren ajiye motoci da kuma gidaje da aka gina na kasa sun cika makil da ruwa yayin da bishiyoyi suka fada kansu, a cewar ma’aikatar kashe gobara.

Ma'aikatan agajin gaggawa sun ceto mutane a cikin motoci a wasu manyan hanyoyi da na karkashin kasa.

A wani yankin, motocin da ke tsaye sun nutse, kuma wasu titunan ba a iya wucewa ta kansu sai dai ta jirage ruwa na roba.

Masana sun ce matsalar yanayi na kara tsananta karfin ambaliya da ake fuskanta.

A shekarar 2021, yankunan yammacin Jamus na Rhineland-Palatinate da North Rhine-Westphalia sun fuskanci mummunan ambaliyar ruwa da ta yi sanadiyar mutuwar mutum sama da 180.

TRT World