Billal yana samun natsuwa a masallacin Kaya a lardin Aksaray a Turkiyya bayan ya yi sallar azahar. Hoto: Billal Higo      

A lokacin annobar korona a watan Disambar 2020, Billal Higo ya shigo jirgi daga Munich zuwa Istanbul lokacin da tunanin abin ya bijiro masa.

Billal yana so kashe kishirwar bukatarsa da karuwar imaninsa. Shawarar da yanke ta kai ziyara masallatai ya yi tasiri sosai a rayuwarsa, wannan yana nuna yadda ya sauya sana'arsa a fannin sufurin jirgin sama zuwa abin da yake kauna da kuma karuwar imani.

Zaune a jirgi zuwa Istanbul, Billal ya tambayi kansa cewa, "Masallatai nawa ne zan iya yin sallah a ciki yayin wannan tafiya?"

“Sai na ga idan na yi sallar farilla daya a jam'i a masallaci daya a kwana 21, to na yi na yi sallah kenan a masallatai 105 jumulla," kamar yadda Billal ya shaida wa TRT World.

Ya samu kawarin gwiwa ne daga Hadisin Manzon Allah (SAW) ya ce ne, "Ka kasance a duniya kamar bako ko matafiyi," Billal ya shirya tafiyar addini don gano bambance-bambancen da ke tsakanin Musulmi ta hanyar tafiyarsa a fadin duniya.

Labarin Billal ya kasance mai karfafa gwiwa ga wasu yayin fara wani taro kan aikin Hajji – wani lokaci da miliyoyin Musulmi suke zuwa Makkah don yin ibada da neman gafara da kuma samun hadin kai da 'yan uwansu Musulmi maza da mata.

Mahukuntan Saudiyya sun ce akalla mutum miliyan biyu ne suke sauke aikin Hajji a bana wanda aka fara a wannan Litinin din.

Daya daga manyan taron addini da ke samun halartar dimbin mutane, a bana kamar yadda aka saba ya samu halartar jama'a da yawa, bayan shekara uku da aka takaita adadin masu ibada saboda annobar korona.

Tafiya zuwa Istanbul

Ya fayyace girman abin da ya sanya a gaba, Billal ya aika wa abokin tafiyarsa Karim sako wanda yake cikin wani jirgi daga Berlin zuwa Istanbul.

Rufe masallatai da aka yi na wucin gadi ya yi tasiri sosai ga dimbin Musulmi, ciki har da Billal.

Kafin annobar korona, yana amfani da lokacinsa wajen shiga mutane da salloli da kuma karatu a masallatai.

Ya karanta fannin Al'ada da Dabi'ar dan Adam a makarantar London School of Economics kuma ya kammala nazarinsa ne a shekarar 2021 a kan 'al'ada da kalubalen asalin mutane masu addinai a a kasar Jamus'.

Yana kwashe lokaci yana nazarin maudu'in a masallaci.

'Kara cika imaninsa'

Tafiyar mako uku da Bilal ya yi zuwa Turkiyya ta bayyana yadda yake so "ya sake kara cika imaninsa."

"Wannan ne lokacin farko da na kudiri niyyar yin sallah duka ko kuma duka sallolina a masallaci," in ji ta, ya jaddada muhimmancin fahimtar wuraren ibada da rungumar bambance-bambancen da ke tsakanin Musulmin duniya da zuciya daya.

Masallacin Omer Ibn el-Hattab a birnin Sarajevo shi ne masallaci na 100 da Billal ya yi sallah kuma ya kammala babban aikin da ya sa a gaba na farko. Hoto: Billal Higo

Tafiyar ta yi tasiri sosai a rayuwata in ji Billal, wanda yanzu yake aiki mai bai wa jama'a shawara kuma mai nazari da bincike kan dabi'ar dan Adam.

Fiye da shekara biyu da suka wuce, Billal ya kai ziyara kasashe 19 – daga Turkiyya zuwa Afirka ta Kudu.

A kan hanyarsa ya kai ziyara Bosnia da Tajikistan da Kyrgyzstan da Uzbekistan kuma ya je Masar da Saudiyya.

Sanadin tafiye-tafiye, Billal "yana so ya san kuma ya fahimci bambance-bambancen da ke tsakanin Musulmai a bangarori daban-daban na duniya ta hanyar kai ziyara masallatai da kuma fahimtar al'adu daban-daban."

Inda ya fara yada zango: Masallacin Blue Mosque da ke Istanbul

Yayin tafiyarsa daga Istanbul, Billal da abokinsa Karim ta kama hanyar tafiya inda suka fara daga Masallacin Blue Mosque mai tarihi, wani wajen ibada na Daular Ottoman wanda yake da hasumiya shida wanda Sarki Ahmed I ya kammala gina sa a shekarar 1616.

Daga nan tafiyarsu ta kasa ta kai su lardunan Turkiyya da ba a fiye ganin masu yawon bude ido ba kamar lardin Bilecik da Afyon da Aksaray da kuma Zonguldak, inda suka rika kai ziyara masallatai a duk inda suka tsaya.

Sun kammala babban aikin da suka sa gaba ne ta hanyar yin sallah a masallacin Omer Ibn el-Hattab wato masallaci na 100 kuma na karshe a aikin da suka sa gaba, a birnin Sarajevo a kasar Bosnia.

Yayin da aka tambaye shi ko wane masallaci ne ya fi burge shi, ya bayar da amsar da ta ba da mamaki. Ba Masallacin Ayasofya ko Suleymaniye ba ne.

Ba kuma masallaci ne da aka mai gini salon hasumiyar Daular Ottoman mai tayal shudi ba ne, ba kuma masallacin Anatolian Seljuk da aka yi wa ado da katako ba ne.

Bilal ya ce masallacin da ya fi burge shi, shi ne wani karamin masallaci a garin Aksaray. An yi amfani da duwatsu wajen gina Masallacin Kaya Camii.

Kaya Camii, wani karamin masallaci ne da ke cikin wani kogo a tsaunin Ihlara. Hoto: Billal Higo 

A wani gandun daji, muna neman masallaci don yin sallar azahar sai muka ga wani masallaci a kusa a manhajar Google Map, daga nan sai ya ga wata alama a duwatsun wadda yake masa nuni da inda masallacin yake.

“Masallaci ne karami, mai sauki, kamar yadda Billal ya tuna. "Ya tuna min da Suratul Rahman, wadda take kwadaitar da masu imani muhimmancin halittun Ubangiji."

Babu wani da yake kusa da zai kira sallah, abokin Billal, Karim sai ya shige gaba ya kira sallah.

Abokan biyu sun yi jam'i tare, a wannan karon bishiyoyi da dutwasu da tsaunuka su ma da su aka daidaita sahu.

“Ba zan taba mantawa da wannan masallacin ba," in ji shi.

Farko sabon kalubale

Billal ya fara tafiyarsa ne daga Turkiyya zuwa Bosnia a farko. Daga nan ne sai ya tasa wani sabon babban aiki a gaba, inda ya fara kai ziyara masallatai a kowace wurin da ya je.

Yayin da ya kai ziyara Afirka ta Kudu, Billal ya yi sallah a cikin wani masallaci a Robben Island kusa da Cafe Town, inda Nelson Mandela ya kwashe shekara 18 cikin shekara 27 na zaman gidan yarin da ya yi, sai bayan kawo karshen mulkin nuna wariyar launin fata inda daga baya ya zama shugaban kasa.

Wani masallaci a Robben Island kusa da Capetown wajen da mutum da ya lashe kyautar zaman lafiya ta Nobel, Nelson Mandela ya yi shekara 18 cikin shekara 27 da ya yi a tsare. Hoto: Billal Higo

Yayin kowace tafiya, Billal ya ga abubuwa iri-iri dangane da al'adun Musulunci, inda yake salloli biyar a cikin jam'i a masallatai daban-daban, ya gana da mutane kuma ya ga yadda suke ibada a addinin Musulunci.

“Na lura cewa duk lokacin da na yi kokarin mayar da hankali kan masallatai da jama'arsa. Hakan ya sa na fahimci kasar da al'adunsa ta daya bangaren," in ji Billal.

Tajik wurin karamci

A kowace kasa da ya ziyarta, jama' a sun karbi Billal hannu biyu-biyu inda suka yi maraba da shi a matsayinsa na Musulmi dan uwansu.

“Yayin da nake masallaci, idan mutane suka ganni ina sallah saboda ina da tsawo da kuma fatata tana da duhu saboda mutane suna ganina kai-tsaye.

A masallacin mutane ba sa yi mini kallon wani mutum da yake da daloli ko dan yawon bude ido. Suna cewa ne wannan dan uwanmu ne, wani mutum ne da yake ibada tare da mu."

Masallacin Juma da aka gina a karni na 16 wanda aka kawata shi da katakana 213 a Khiva a kasar Uzbekistan. Hoto: Billal Higo

Ya kuma tuna yadda aka tura masa dimbin gayyata daga mutane daban-daban, sai dai ya ce akwai wata gayyata da aka aiko masa wadda ba zai manta da ita ba.

Yayin da yake Tajikistan, ya hadu da wani mutum mai suna Jakha a wani masallaci wanda ya gayyace shi zuwa gidansa. Sai dai Billal bai san cewa gayyatar za ta kai shi wani kauye mai nisan tafiyar minti 40 daga masallacin.

Ya bayyana yadda zantawarsu ta kasance, Billal ya ce, "Yayin da na isa kauye, na gane cewa wata rayuwata ce ta daban a wani karamin gari. Duka iyalan Jakha suna rayuwa a wani titi daya."

“Na je gidan Jakha kuma makwabtansa sun zo sun kasance da mu. Mun ci abinci tare, mun san juna kuma mun yi barci a gidansu. Har yanzu muna magana da shi da iyalansa."

‘Kalubalen ziyarar masallatai 100’

Aiki da Billal ya sa a gaba na kai ziyara masallatai 100 manuniya ce ga 'yan uwanta da ya rasa kasashe da al'adu da harsuna.

Yayin da aka tambaye shi kan abin da ya fi muhimmanci da ya koya daga tafiye-tafiye da ya yi, sai Billal ya ce, "Za ka ga bambance-bambancen iri-iri idan ka neme su.

Duk san da ka fara mayar da hankalinka kan abubuwa da suke kama da juna, za ka samar da yarda, da zarar ka samar da yarda to karin mutane za su fara gayyatarka zuwa kusa da su, kuma wannan ne wuri da ya fi dacewa ka fahimci al'adunsu. Ina ganin wannan ne abin da yake bude maka kofofi."

Billal ya ce saboda tsawonsa da yadda ya fita daban hakan ya sa yana jan hankalin mutane musamman a yankin Tsakiyar Asiya, abin da yake jawo mutane suke bukatar da su dauki hoto tare. Hoto: Billal Higo

Duk tsawon lokacin da ya kwashe yana tafiye-tafiyen, ba a rika la'akari da kasarsa ko launin fatarsa ba, amma an fi mayar da hankali ne kan kasancewarsa Musulmi, in ji shi.

Ya ce abubuwan da ya fahimta daga tafiye-tafiye abubuwa ne da ya koye su daga Al-Kur'ani (49:1: "Ya kai dan Adam, hakika mun halicce ku maza da mata kuma muka yi ku zuwa kalibu daban-daban don ku fahimci juna."

Ya ce huldarsa da mutane daga mabambantar wurare ya kara karfafa alakarsa da Mahaliccinsa kuma ya kara tabbatar da maganar Al-Kur'ani cewa ta hakan yana sa ku san juna kuma ku fahimci juna.

“A shekarar 2024, ya ce yana fatan kai wa kololuwar aikin da ya sa a gaba kuma ya ce zai rika wallafa bayanan tafiyarsa a shafinsa na Instagram," kamar yadda Billal ya ce cikin farin ciki, ya ce a shirye ya ci gaba da tafiye-tafiye da kuma gano wurare da ba zai iya mantawa da su ba.

TRT World