Kungiyar Kula da Al'amuran Musulunci na Turkawa (DITIB) ta ce wasu mutane sun kona Alkur'ani Mai Tsarki tare da jefar da shi a gaban wani masallaci a kudu maso yammacin Jamus.
Lamarin ya faru ne a gaban Masallacin Mimar Sinan a garin Maulbronn, da ke Jihar Baden-Wurttemberg, daga cikin wata mota da ke tafiya.
Osman Adibelli, daraktan kungiyar masallacin ya ce abin ya faru ne a ranar Asabar 8 ga watan Yuli.
"Bayan faruwar lamarin, da muka duba bidiyon da kyamarar tsaro ta dauka ta masallacinmu, mun ga yadda aka wurgo da wani abu daga cikin wata mota a kan titi. Da misalin karfe 4.45 na asuba, sai mutane da suka fito sallar Asuba suka fahimci cewa an kona Kur'ani ne a kofar shiga masallacin," ya fada a cikin wata sanarwa a ranar Litinin.
Adibelli ya ce sun shigar da korafi kan lamarin kuma "saboda wutar gaban motar ta haske sosai ba mu iya gane lambar motar ko yawan mutanen da suka aikata hakan ba."
Da yake bayyana kaduwarsa kan lamarin, Adibelli ya sanar da cewa tuni aka kaddamar da bincike.
Lamarin na zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da kona Kur'ani a wasu kasashe da dama na nahiyar Turai, ciki har da wani da aka yi a wani masallaci a Sweden, da 'yan sanda suka ba da izinin yi, wanda ya jawo ce-ce-ku-ce sosai a fadin duniya.
Jagororin Musulmai da 'yan siyasa sun yi ta nanata cewa irin wannan lamari ba 'yancin fadin albarkacin baki ba ne.