Masu tsaurin ra'ayi na yawan kai wa masallatai hare-hare a Jamus / Photo: AP

An aike wa wani masallaci a birnin Dusiburg da ke tsakiyar Jamus wasika mai cike da barazanar nuna wariyar launin fata, a cewar wani jami'in kula da harkokin addinai.

Babban Masallacin na Duisburg wanda ke da alaka da Kungiyar Turkawa Musulmai ta DITIB, ya ruwaito cewa wasikar na dauke da tambarin mabiya Nazi da kuma rubutun ‘NSU 2.0’, wanda alama ce ta wata kungiyar 'yan Nazi da aka san ta da aikata kisan gilla.

Ba tare da bata lokaci ba masallacin ya aika wa 'yan sanda wasikar tare da shigar da korafi. Yusuf Aydin shi ne shugaban Babban Masallacin Kungiyar DITIB, ya bayyana bacin ransa a kan lamarin tare da neman a yi gaggawar gabatar da masu laifin a gaban kuliya.

Jamus mai yawan al'umma fiye da miliyan 84, ita ce kasa ta biyu da ta fi yawan Musulmai a Turai baya ga Faransa. Musulmai kusan miliyan biyar ne ke zaune a kasar, a cewar alkaluman hukumomi.

Sannan akwai Turkawa miliyan 3.5 'yan asalin Turkiyya a Jamus, inda a nan ne suka fi yawa a Turai.

Aydin ya ce ba wannan ne karo na farko da aka aike wa masallacin sakon barazana ba, an kai a kalla irin wannan sako sun kai 12 a baya.

A wani lamarin daban kuma, Ofishin Watsa Labarai na Kungiyar DITIB ya ruwaito cewa an lalata wata tutar Turkiyya da aka kafa a Masallacin Selimiye a Bremen, inda aka gano wanda ya aikata haka din dan kungiyar ta'addanci ta PKK ce.

Lamarin ya faru ne yayin da ake cin wata kasuwa ta mako inda aka lankaye tutocin Turkiyya da Jamus da na Kungiyar DITIB a kan katangar masallacin. Maharin ya cire tutar Turkiyyan ya yaga ta sannan ya gudu ya bar wajen.

Hidayet Tekin, shugaban Kungiyar Masallacin Bremen Selimiye, ya bayyana kaduwarsa kan alakar maharin da kungiyar PKK sannan ya jaddada muhimmancin tabbatar da tsaron masallacin.

Tekin ya ci gaba da bayyana cewa maharin ya kuma yada bidiyon harin a shafukan sada zumunta, inda ya nuna yadda ya fatattaka tare da kona tutar Turkiyyan a wani wajen ajiye motoci.

Ana nuna damuwa kan yadda kin jinin Musulmai ke karuwa da kai hare-hare, lamarin da ke yin babbar barazana ga al'ummar Musulmai da suke zaune a kasar.

Babban abin damuwar shi ne yadda ba a mayar da hankali wajen yin bincike kan irin wadannan abubuwa da suke faruwa, inda hakan ke kara saka Musulmai cikin barazana.

Musulmai suna sallah a wani sabon masallaci da aka gani a Duisburg

An hai hari kan masallatai fiye da 800 tun daga 2014

A wani rahoto da wata kungiya ta masu sassaucin ra'ayi Brandeilig ta fitar kwanan nan, ta yi karin haske kan karuwar barazana da hare-hare da ake kai wa masallatai a Jamus.

Sai dai kuma, mafi yawan wadannan laifuka ba a bincike sosai a kansu, inda masu aikata hakan suke ci gaba da cin karensu ba babbaka tare da ci gaba da kai hari wuraren ibadun Musulmai.

Brandeilig, wadda ta fara samar da cibiyar kai rahotannin hare-hare kan masallatai, ta tattara bayanai kusan 840 na irin wadannan hare-hare da suka faru daga tsakanin shekarar 2014 da 2022.

Bayanan, wadanda aka samo daga wani sharhi da aka gudanar a 2018 sun fayyace cewa tara daga cikin hare-hare 120 ne kawai aka gano wadanda suka aikata su.

Wannan rashin gano masu laifin shi ke kara sanya al'ummar Musulmai cikin matsi tare da bai wa masu akidar Nazi da masu tsaurin ra'ayi damar ci gaba da kai hare-hare kan masallatai.

Rahoton DITIB

Al'amuran da suka faru a Duisburg da Bremen sun fito da irin kalubalen da masallatai ke fuskanta a Jamus.

A cewar wani rahoto da Kungiyar DITIB ta fitar kwanan nan, a kalla masallatai 35 aka kai wa hari a 2022, inda kin Musulunci ne ya sa masu tsaurin ra'ayin ke kai hare-haren.

Ofishin da ke kula da yaki da wariya na DITIB ya fitar da wani rahoto kwanan nan mai shafi 32 da ke bayani a kan kiyayya da barazana da hare-haren da ake kai wa masallatai da kungiyoyin Musulmai a Jamus a 2022.

A cewar kwararru na kungiyar DITIB, kiyayyar da ake nuna wa Musulmai na da alaka da zamantakewa da siyasa da kuma muhawarar da ake yi a kan 'yan cirani da Musulmai da Musulunci.

TRT World