Gwamnati ta ce za ta yi nazarin rahoton sosai tare da duba shawarwarin da ya bayar don daukar mataki  / Photo: AP

Musulmai na fuskantar tsananin wariya da matsin lamba a Jamus nuna musu tsana, abin da ke nuna ya kamata a dauki matakan dakile hakan, a cewar wata hukuma mai zaman kanta da gwamnati ta ba ta aikin tattara bayanai kan hakan.

"Mafi yawan Musulmai miliyan 5.5 na Jamus na fuskantar wariya a kowace rana a rayuwarsu — da tsana da ma kai musu hari," in ji Ministar Harkokin Cikin Gida Nancy Faeser a ranar Alhamis bayan karbar rahoton.

Ta yi alkawarin cewa gwamnati "za ta yi nazarin rahoton sosai tare da duba shawarwarin da ya bayar" sannan ta yi yaki da nuna wariya da kuma kare Musulmai daga nuna musu kiyayya.

Hukumar mai mambobi 12 ta ba da misali da bayanan da ke nuna yadda kusan duk Jamusawa ke goyon bayan kalaman kin jinin Musulmai, "abin da ke jawo yanayin da ka iya samar da kungiyoyin masu ra'ayin rikau.

Ko Musulman da aka haifa a Jamus ma ana musu kallon baki, yayin da ake yawan danganta Musulunci da "addinin da ya ci baya" sannan mata masu sa mayafi sun ma fi fuskantar matsalar.

A wani sharhi kan wata sananniyar al'ada da aka yi, rahoton ya gano cewa kashi 90 cikin 100 na fina-finan da mambobin kwamitin suka kalla, duk marasa dadi ne a Musulmai, inda ake yawan alakanta su da "hare-haren ta'addanci, da yake-yake da musgunawa mata".

Kin Musulmai da kai musu hari

Jam'iyyar AfD ta masu ra'ayin rikau, wacce a yanzu take da kashi 20 a fadin kasar, tana matukar nuna goyon bayan kin jinin Musulmai.

Hukumar ta ba da shawarar kirkirar wata kungiya da za ta magance matsalar nuna wa Musulmai wariya, inda za ta dinga tattara korafe-korafe.

Sannan, ta ce za a dinga bayar da horo a cibiyoyin kula da masu rauni da makarantu da ofisoshin 'yan sanda da ofisoshin gwamnati da kafafen watsa labarai don dakile irin kallon da ake yi wa Musulmai.

Ta ce alkaluman aikata laifuka sun fara nuna ainihin abin da ke faruwa na hare-haren kin jinin Musulmai, amma kuma har yanzu akwai sauran abubuwan da ke faruwa ba a ba da rahotonsu.

A shekarar 2020 ne tsohon Ministan harkokin cikin gida na Jamus Horst Seehofer ya kaddamar da hukumar, bayan da wani mai tsaurin ra'ayi ya kashe mutum 10 tare da raunata wasu biyar din a wani harin kin jinin Musulmai da ya bude musu wuta a birnin Hanau.

Harin ya girgiza kasar tare da jawo hankulan kungiyoyin kare hakkin dan adam kan karuwar kin jinin Musulmai a Jamus.

Kazalika a wani rahoton na daban da aka fitar a ranar Talatar da ta wuce, wata kungiya da ke sa ido ta ce laifuakn kin jinin Yajudawa ma na karuwa a Jamus, inda aka samu rahotannin hare-hare har 2,480, inda ya ragu da kashi daya a shekarar da ta gabata.

TRT World