Baptiste Devis, daya daga cikin 'yan kwana-kwanan da suka je wurin, ya ce lokacin da suka isa ginin wutar da ke ci a cikinsa ta kai tsaron mita 5 zuwa 6 (kafa 16-20).  FILE PHOTO

Ana ci gaba da jinjina wa wani matashi Musulmi wanda ya yi kundumbala ya shiga wani gida da ke ci da wuta sannan ya ceto mutum 17, cikin har da jariri.

A cewar gidan rediyon France Bleu, gobara ta tashi ranar Juma'a a wani gida mai hawa biyu a Romans-sur-Isere da ke kudu maso gabashin Faransa.

Matashin mai suna Izzeddin Hamdi, wanda ke tallan biredi a yankin lokacin da gobarar ta tashi, ya ruga a guje cikin ginin inda ya ceto mutum 17, ciki har da jariri, kafin 'yan kwana-kwana su isa wurin.

Hamdi ya yi amfani da tsani ya shiga gidan ta wata taga duk kuwa da wutar da ke ci ranga-ranga da kuma hayakin da ya turnuke.

Mutane sun rika jinjina wa Hamdi suna kiransa gwarzo yayin da masu amfani da Twitter a kasar suka rika yin kira a karrama shi lambar yabo mafi girma a kasar wato Legion of Honor.

Baptiste Devis, daya daga cikin 'yan kwana-kwanan da suka je wurin, ya ce lokacin da suka isa ginin wutar da ke ci a cikinsa ta kai tsaron mita 5 zuwa 6 (kafa 16-20).

AA