An aika wa wani masallaci a Jamus wasikar da ke barazana ga Musulmai, in ji wani jami'i.
An tura wasikar ce zuwa Masallacin Eyup Sultan da ke garin Bramsche da ke jihar Lower Saxony ranar Juma'a.
"Ku ci gaba da abin da kuke yi. Za mu yi muku abin da muka yi wa Yahudawa. Za mu yi haka ne nan ba da jimawa ba," a cewar wasikar.
Kazalika wasikar na dauke da kalamai na zagi ga Musulunci.
Ahmet Irmak, shugaban masallatan da ke da alaka da kungiyar Turkish-Islamic Union for Religious Affairs (DITIB), ya ce a farkon makon nan an aika wa wani masallaci irin wannan wasika.
An rufe wasikun sannan aka sanya musu tambarin NSU 2.0, wata alama ta 'yan Nazi da suka dauki alhakin kashe-kashe da dama.
Yawaitar kai hare-hare a masallatan Jamus
Irmak ya kara da cewa an tura musu irin wannan wasika ta imel kusan shekara guda kenan.
Ya bayyana damuwa kan irin wannan barazana sannan ya yi kira ga hukumomi su sanya ido sosai.
Ya ce sun kai rahoton wannan lamari ga 'yan sanda.
An kai hari sau akalla 35 a masallatan Jamus a bara, kuma galibinsu masu tsananin kyamar Musulunci ne suke kai su, a cewar DITIB.
Kungiyar Brandeilig da ke da alaka da kungiyar kare hakkin dan adam ta FAIR International, ta ce an kai hari akalla 840 kan Musulmai daga 2014 zuwa 2022.
Irin wannan barazana na zuwa ne makonni bayan wasu makiya Musulunci sun kona Alkur'ani mai tsarki a kasashen Sweden da Denmark, lamarin da ya jawo kakkausar suka daga kasashen Musulmai a fadin duniya.