Kasashen yankin arewacin Afirka da dama ciki har da Masar na daga cikin wuraren da a halin yanzu ke fuskantar matsanancin yanayin zafi. Hoto: AA

Sakamakon tsananin yanayin zafi da ake fama da shi a yankunan kasashen Asiya da Arewacin Afirka da Turai da kuma Amurka, mutanen da ke wadannan wuraren sun dauki salo da dabarun sanyaya jikinsu don rage radadin yanayin da ake ciki.

Kasar Moroko da Masar da kuma Aljeriya su suka fi fuskantar yanayin zafin a yankin Afirka.

Dukka kasashen uku suna fama da mummunan yanayin da ke haifar da fargaba da damuna kan matsalolin kiwon lafiyar jama'a.

A cikin watan Yuli an samu ranar da ta fi ko wace rana zafi a duniya. Hoto: AA

Jama'a sun haifar da cunkoson a bakin teku da ke kudancin Turai da Amurka inda aka yi hasashen samun zazzafan yanayi a cikin kwanaki masu zuwa.

Hukumomi sun ba da shawara kan a yawaita shan ruwa sannan mutane su guji shan barasa da gahawa domin suna rage ruwan jikin mutum.

Hukumomi sun yi gargadi game da mumunar yanayin zafi da Italiya ke fama da shi inda yanayin ya haura maki sama da 45 . Hoto: Reuters

A Italiya, hukumomi sun shawarci al'umma da su kula da tsofaffi saboda tsananin zafi.

Falasdinawa a Gaza suna ta kai ziyara gabar teku don sanyaya jikinsu, yayin da iyaye ke zuba wa yara ruwa ta bututun ruwa sakamakon yanayin matsanancin zafin da ake ciki.

Yara da tsofaffi na daga cikin wadanda suka fi fuskantar matsanancin yanayin da ake ciki . Hoto: AA

Tsananin zafi na kara haifar da kalubale ga iyalai marasa galihu wadanda ke zaune a gidaje na wucin gadi a Gaza.

Fiye da mutum miliyan 2.3 ne suka mamaye zirin Gaza, Unguwar al-Nasr tana da mutanen masu yawan gaske da ke zaune a gidajen na wucin gadi kuma ba su da halin iya sayen na'urorin sanyaya gida.

Mazauna yankin da dama suna zama a waje tare da neman ruwa da za su yi amfani da shi don jure yanayin zafin.

Unguwar al-Nasr da ke cikin birnin Gaza na da mutane da ke zaune a gidaje na wucin gadi. Hoto: AA

Yankin Allahabad na kasar Indiya ya kasance wuri da ya fi ko ina fama da zafi a kasar. Maza na shafa laka a jikinsu don sanyaya jikinsu a gabar Kogin Ganges.

Wasu mutane a Indiya na bin hanyoyin na daban don sanyaya jikinsu yayin da kasar ke fama da mumunar yanayin zafi a yan shekarun nan. Hoto: AA

An yi hasashen yanayin zafi a Allahabad zai kai maki 44 a ma'aunin Celsius wato (digiri 111.2 Fahrenheit), a cewar shafin yanar gizon na sashen kula da yanayi a Indiya.

Guguwar zafi ta tilasta wa mutane canza yanayin salon rayuwarsu inda suke nishadantar da kansu a kokarin neman mafiya Hoto: AA

Masana sun ce guguwar zafi da ta mamaye kasashe da dama a duniya wata alama ce ta barazanar dumamar yanayi.

TRT Afrika