Ba bakon abu ne ganin konawa da cin zarafin Alkur'ani Mai tsarki a Sweden da wasu sassan Turai. A can baya, kona litattafai masu tsarki irin wannan wulakanci ya yi kamari, har ya shafi abubuwan da ba ma rubututattu ba.
A ra'ayin Dr Farid Hafez, babban mai bincike a Cibiyar Bridge ta Jami'ar Georgetown, ana kona litattafai masu tsarki ne don cin fuskar mutanen da ke da dangantaka da littafin a lokacin da ba sa nan ko bayan sun mutu, sai a lalata abin da yake wakiltarsu.
Ya ce "A ra'ayina, kona litattafai kisan kai ne ko rusa wani da ba ya nan ne, a lokacin da aka gaza kashe wadannan mutane da suke girmama littafin."
A lokacin da yake bayanin tarihi kan abubuwan da suka faru a Sifaniya, Dr Hafez ya ambato marubuci dan kasar Jamus Heinrich Heines da ke cewa 'Wadanda suke kona litattafai za su iya kona mutane'.
A lokacin sarkakiya a Sifaniya a shekarun 1500, Shugaban Kiristoci Ximenez Cisneros ya bayar da umarni ga jama'a da su kona duk wasu litattafai na Larabci da suka samu a Granada. Sai dai ya ce a bar wadanda suka shafi likitanci. Bayanai sun nuna cew an kona litattafai akalla 5,000.
Kwararru da masu nazari sun bayyana cewa ya kamata a kalli ayyukan kona Alkur'ani ta mahangar tarihi saboda yadda a baya irin wannan abu ya janyo tashin hankali da rikici wajen murkushe marasa rinjaye da masu rauni a tsakanin al'ummu.
Tarihin kona litattafai a Turai
"Kona litattafai masu tsarki kamar Alkur'ani - ko Attaura - laifi ne na nuna kyama," in ji Lena Posner shugabar Yahudawan Sweden - Korosi a yayin wata tattaunawa.
Tunatarwa ce mai muhimmanci ga jama'arta saboda yadda hakan ya sanya su tunawa da tsarin Nazi na kona litattafan Yahudawa, wanda hakan ne mafarin yi musu kisan-kiyashi.
Daga Mayun 1933, kungiyoyin dalibai karkashin Nazi sun dinga shirya tarukan wuta inda suke kona litattafan da ba na Jamus ba. Wadannan kone-kone sun afku a garuruwa da birane 34, da ma jami'o'i. An kona litattafan marubuta Yahudawa da dama.
Sakamakon hakan ne ya sanya al'ummun Yahudawa da ke Sweden da Denmark suke neman mahukunta da su dauki tsauraran matakai don magance wannan aika-aika, "Tarihi ya koya wa Yahudawa darasi kan me zai iya biyo baya idan aka fara kona litattafai," in ji Posner-Korosi.
Tana kira da a yi kwaskwarima ga dokokin da ake da su a yanzu game da laifukan nuna kyama ta yadda za a haramta kona litattafai masu tsarki.
Rashid Musa, tsohon shugaban Kungiyar Matasan Musulman Sweden, na tunanin akwai bukatar a yi la'akari da tarihi kan abubuwan da suke afkuwa a yanzu haka.
Musa ya ce "Mahukuntan Sweden na amfani da batun 'yancin bayyana ra'ayi don ba shi (Paludan) damar kona Alkur'ani, amma ya kamata mu fahimci wannan sannan mu dora shi a kwarya ta tarihi.
Ya kara da cewa "Ba sai mun je da nisa ba inda za mu iya kallon Bosnia a tsakiyar shekarun 1990, inda Sabiyawa masu nuna wariya suka fara da kona litattafan adabi na Bosnia tare da dasa bama-bamai a dakunan karatu."
A watan Agustan 1992, mummunan abu ya afku a Sarajevo, babban birnin Bosnia, inda da gangan aka kona kusan litattafai miliyan biyu. Wannan mummunan lamari ya janyo an kona litattafai da dama da aka rubuta a zamanin Daular Usmaniyya, da kuma litattafai masu shekaru 500 da ke ajiye a dakin karatu na kasa ta Bosnia da Herzegovina.
Biyu daga cikin wadannan munanan ayyuka na kisan kiyashi, sun faro ne tare da ganin kona litattafan da suke da girma ga wadanda aka kashe din.
Idan aka kyale abin a haka, kwararru sun ce za a iya samun mummunan sakamako, wanda ke yin barazana ga rayukan Musulmai da yawa da suke rayuwa a Turai da ma wajen nahiyar.
Rashin hukunta 'Laifin Nuna Kyama'
Har yanzu ana ci gaba da ganin mummunan tasirin rikicin da aka yi a Turai, tare da karuwar masu tsaurin ra'ayi da ke yada nuna wariya a duniya baki daya, kuma suke kutsawa fagen siyasa tare da samun wajen zama. Wannan ta'ada ta kara rura wutar aikata laifukan nuna kyama a nahiyar.
Jam'iyyu masu ra'ayin rikau sun taba zama kusan a gaba-gaba a fagen siyasa, a yanzu na samun mukamai a gwamnati tare da sauran jama'a masu saukin ra'ayi, kamar yadda ake gani a kasashe da dama.
A Finland, misali, jam'yyar "Finns", tare da rinjayen nuna kyama da masu gudun hijira da adawa da ra'ayin Tarayyar Turai, kwanan nan ta samu damar shiga gwamnatin hadaka a kasar. Haka kuma a Italiya da Sweden an ga irin wannan abu, inda masu tsaurin ra'ayi suka shiga gwamnatin hadaka a kasashen.
A wani bayani na Tarayyar Turai a 2021 mai taken "Turai Mai Tsaro da Tafiya da Kowa: Bayyana laifuka da kalaman nuna kyama" an bayyana karuwar kalamai da nuna kyama a Turai.
Kwamitin kaddamar da wannan takarda ya bayyana cewa "Ana nema a sabunta nuna tsana, ana nufar daidaikun mutane da kungiyoyi da aka ga suna da wasu kamanceceniya kamar na launin fata, yare, kabila ko addini."
Matukar shahararrun 'yan siyasa za su dinga nufar wasu mutane da kalaman nuna kyama, to lallai za a ci gaba da ganin hakan kuma zai zama ba komai ba a tsakanin jama'a.
Ta'annatin kona Alkur'ani Mai Tsaki, wanda shugana jam'iyyar masu tsaurin ra'ayi a Denmar ya kara fito da shi sosai, ya zama misali mummuna na nuna wannan ta'nnati ba komai ba ne.
Ana ta ganin afkuwar wannan ta'annati, a Turai da wasu sassan duniya, wanda ke nuna ci gaba da nuna kyama ga Musulmai.
Kona Alkur'ani Mai Tsarki: Daga Amurka zuwa Turai
A 2015, a kurkukun Guantanamo Bay inda ake tsare da daruruwan Musulmai saboda manufofoin Amurka kan ta'addanci a duniya, bayan harin 9/11, an ba da rahoto da ke nuna yadda wasu jam'ian Amurka suke muzanta Alkur'ani tare da zuba shi a masai, kawai don su bakanta wa Musulman da ke daure.
A yayin tunawa da harin 9/11 a karo na tara, wani Fasto mai suna Terry Jones ya sanar cewa zai kona kwafi 200 na Alkur'ani Mai tsarki. Cocinsa ya kuma yi shirin karbar bakuncin 'Ranar Kona Alkur'ani ta Duniya' amma daga baya ya soke hakan saboda tsanantar zanga-zanga.
Duk da soke shirinsu na farko, Jones ya sake kokarin shirya taron kona Alkur'ani a ranar 11 ga Satumban 2013. Amma an kama shi kafin ya kona kwafi 2,998 na Alkur'ani, wanda kowanne daya ke nufin mutum guda da ya mutu a harin na 2001. An tuhumi Jones da laifukan safarar man fetur da daukar harsunan wuta.
'Yan siyasar Turai da suke ingiza wannan aika-aika, suna zagin Alkur'ani da Musulmai. A 2017, Geert Wilders wani dan siyasar Holan mai tsaurin ra'ayi, ya yi barazanar haramta karanta Alkur'ani a kasar, inda yake kwatanta shi da littafin Adolf Hitler na 'Mein Kampf'.
A 'yan shekarun nan, Rasmus Paludan wani mai tsokana dan kasashen Denmark da Sweden, ya sake farfado da kona Alkur'ani Mai Tsarki. Wannan ta'annati da ya yi ya sake ingiza masu neman suna a duniya inda suke bin sawunsa. Suna amfani da hanyar da yake bi, Paludan kuma ya koyi wannan aibu daga mutane irin su Wilders, yana bayyana kansa ga duniya.
"Yancin bayyana ra'ayi ko nuna kyama?
Muhawarar da ake yi a Turai game da kona Alkur'ani Mai Tsarki ta fi mayar da hankali kan kare 'yancin bayyana ra'ayi, maimakon magance nuna wariya da kona Alkur'anin. Wannan abu na iya ta'azzara yadda ake ci gaba da amincewa da wannan dabi'a ta kyamar Musulmai.
Da aka tambaye shi ko gyara dokokin Turai ta yadda za a bayyana kona Alkur'ani Mai Tsarki a matsayin wani babban laifi na nuna kyama da za a dinga hukunta masu aikata shi don tabbatar da bayar da kariya ga Musulmai, Dr Hafez ya bayyana damuwa sosai kan wannan.
"Idan kona Alkur'ani na nufin kisa ta hanyar wakilci, musamman a wajen mutanen da ke alakanta kawunansu da fifikon farar-fata, to tambayar da za a yi ita ce ta yaya za mu rayu a duniyar da ake kallon Musulmai a matsayin marasa rinjaye kuma ake nuna musu wariya sannan su zama kamar kowa, kamar dai a Sweden. Wannan ce tambaya mafi girma a waje na."
Ya yi karin haske kan Nuna Kyamar Musulunci da ya yi katutu a kasashen Turai, inda ya zayyano kalubale da dama da Musulmai ke fuskanta:
"Makarantun Musulmai na fuskantar matsin lamba, an daina bayar da kudade ga kungiyoyi irin su 'Kungiyar Matasan Musulman Sweden', ana hana kungiyoyin Musulmai 'yancin kafa makarantu."
"Wannan ne abin da kasashen duniya ya kamata su magance. Idan muka bar wannan yaki ga gwagwarmaya mara karfi, muka ki ba ta muhimmanci, to muna watsi da asalin matsalolin ne."