‘Yan sandan kasar Sweden sun ce sun bayar da damar a gudanar da zanga-zanga a ranar Sallar Idi inda masu zanga-zangar ke son kona Alkur’ani a wajen Masallacin Stockholm a ranar Laraba.
Sun bayar da damar ne mako biyu bayan da kotun daukaka kara ta yi watsi da batun haramcin da ‘yan sandan kasar suka saka na zanga-zanga bayan da aka kona Littafin Mai Tsarki a wajen ofishin jakadancin Turkiyya a watan Janairu.
Lamarin ya yi sanadin zanga-zanga ta makonni biyu, inda aka yi kira da a kaurace wa kayayyakin Sweden.
Ko a ranar Laraba da ake gudanar da Sallar Layya ma sai da wani dan kasar iraki ya kona Kur’ani a wajen wani masallaci a birnin Stockholm na Sweden din.
Salwan Momika ya fara yin wurgi da Kur’anin ne a kasa kafin daga bisani ya kona shi tare da furta kalamai na wulakanci ga Musulunci.
Lamarin ya faru ne karkashin kariyar da ‘yan sanda suka ba shi a ranar.
Firaiministan kasar Ulf Kristersson ya ce Sweden ta so shiga NATO a baya ko kuma a taronta na gaba a Vilnius a wata mai zuwa, duk da cewa ba lallai ba ne idan hakan zai yiwu zuwa lokacin.
Sweden da Finland sun yi watsi da kungiyar da suka dade cikinta ta ‘yan ba-ruwanmu a bara a daidai lokacin da ake ganiyar yakin Ukraine da Rasha, inda suke neman karin tsaro ta hanyar shiga kungiyar NATO.
Sweden ta saka idonta kan shiga kawancen na NATO a tsakanin 11 zuwa 12 ga watan Yuli inda take samun goyon baya daga wasu mambobi da suka hada da Amurka inda Turkiyya da Hungary duka sun nuna rashin goyon baya kan hakan.