Ma'aikatan agaji suna ta fafatukar ceto mutane daga wurin da aka yi hatsarin jirgin kasa kusa da Balasore, mai nisan kilomita 200 daga babban birni Bhubaneswar,  ranar 3 ga watan Yunin 2023 / Hoto: AFP

Adadin mutanen da suka mutu sakamakon wani hatsarin jiragen kasa da ya auku a jihar Odisha da ke kasar Indiya ya karu zuwa mutum 288, yayin da fiye da mutum 900 suka jikkata sannan wasu da dama ke makale a cikin jiragen, a cewar wani babban jami'i.

Sudhanshu Sarangi, darakta janar na hukumar kashe gobara, ya tabbatar wa kamfanin dillancin labarai na AFP wannan adadi ranar Asabar. Daruruwan mutane sun jikkata sakamakon hatsarin wanda ya faru ranar Juma'a.

Ana sa rai adadin zai karu, a cewar Babban Sakataren jihar Pradeep Jena a sakon da ya wallafa a Twitter.

Ya kara da cewa an tura motoci 200 na daukar gawa zuwa inda lamarin ya faru a lardin Balasore na jihar Odisha da kuma karin likitoci 100, baya ga 80 da aka tura tun da farko.

"Ana ci gaba da aikin ceto a wurin da lamarin ya faru kuma za mu kwashe karin wasu awanni kadan kafin mu gama," in ji Sarangi. "Hatsarin abin takaci ne."

Tun da farko Jena ya tabbatar da cewa "an kai kusan mutum 850 da suka jikkata asibitoci", yayin da ake ci gaba da aikin ceto. Sai dai kakafen watsa labaran kasar sun ce wadanda suka jikkata sun karu zuwa fiye da 900.

Jiragen sun yi hatsari ne ranar Juma'a da misalin karfe bakwai na yamma a agogon yankin lokacin da jirgin Howrah Superfast Express, da ya taso daga Bangalore zuwa Howrah, West Bengal, ya bangaji jirgin Coromandel Express, wanda ya taso daga Kolkata zuwa Chennai. Kazalika hatsarin ya shafi wani jirgin-fito, a cewar jami'ai.

Hotunan da aka wallafa a kafafen watsa labaran kasar sun nuna yadda taragwan jiragen suka manne da juna sannan jini yana kwarara daga jikin mutane da suka makale a cikin jiragen a layukan dogon da ke kusa da Balasore, mai nisan kilomita 200 daga Bhubaneswar, babban birnin jihar.

TRT World