Ana kallon dakatar da kudaden da Trump ya yi umarni da tsoma baki kan harkokin da suka shafi cikin gidansu da 'yancin mulkin kansu.

Daga Emmanuel Onyango

Shugabannin jam'iyyun siyasa masu adawa da juna a Afirka ta Kudu sun nuna hadin kai da babu irin sa don nuna adawa ga umarnin Shugaba Trump, ciki har da kai karar aikata muggan laifukan "cin amanar kasa" ga wata kungiyar kamun kafa da aka fahimci tana da kyakkyawar alaka da gwamnatin Trump.

Dakatar da taimakon na zuwa ne sakamakon takaddamar da ke tsakanin kasashen biyu a 'yan shekarun nan - ciki har da yakin Isra'ila a Gaza, yakin Rasha da Ukraine, da ranar da Afirka ta Kudu ke taka wa a BRICS da G20.

Sai dai kuma rikicin gonaki da filaye ne ya fi zama mashahuri a Afirka ta Kudu.

Kwararru na bayyana cewa a Afirka ta Kudu ana kallon dakatar da kudaden da Trump ya yi umarni da tsoma baki kan harkokin da suka shafi cikin gidansu da 'yancin mulkin kansu.

Ba a bin mamaki ba ne yadda Trump ya bayar da umarnin a daina bai wa Afirka ta Kudu tallafin kudade daga Amurka.

"Idan aka zo batun kare mutuncin kasa duk muna hada kawunanmu. Muna da bambance-bambance, na iya zama kan gonaki ko launin fata da ma duk sauran abubuwa.

Amma idan aka batun kasa, kundin tsarin mulki da dimokuradiyya muna hade kanmu karkashin tutar," Farfesa David Monyae, darakta a Jami'ar Johannesburg ya fada wa TRT Afrika.

Kasa da filaye batu ne mai zafi a Afirka ta Kudu, inda mafi yawan gonaki da filayen da jama'a suka mallaka suke a hannun fararen fata 'yan tsiraru sama da shekaru talatin bayan kawo karshen mulkin nuna wariyar fata.

A makon da ya gabata aka sanar da umarnin na Trump, inda Fadar White House ta ambato sabuwar dokar kasar wadda a karkashinta take cewa gwamnatin Cyril Ramaphosa "na kwace gonaki".

Shugaba Ramaphosa ya musanta ikirarin inda ya ki ya ja da baya game da sabuwar dokar. Pretoria na ta dagewa kan sabuwar dokar ba ta "kwace gonaki" ba ce, tana da manufar "tabbatar da jama'a sun samu gonaki" ta "hanyar adalci."

Gwamnatin ta soki "gangamin bayanan karya da farfaganda" kan dokar. Ramaphosa ya samu goyon bayan jam'iyyun manyan 'yan adawarsa - tsohon shugaban kasa Jacob Zuma da babban dan adawa Julius Malema - kan sauyin mallakar gonaki da filaye.

A majalisar dokoki a wannan makon, jam'iyyar Zuma ta uMkhonto weSizwe (MK) ta zargi Trump da yada ikirarin zaluntar manoma a Afirka ta Kudu.

Mafi yawan gonakin da ba na gwamnati ba mallakin farar fata tsiraru ne a Afirka ta Kudu kuma na saka bakake aikin kwadago.

Jam'iyyar ta shigar da kara ta daban a kotu tana kalubalantar AfriForum, wata kungiyar kamun kafa da ke aiki don kare muradun fararen fata a Afirka ta Kudu, tana mai cewa kungiyar na batar da Amurka game da sabuwar dokar kan kasa.

Jam'iyyar ta zargi kungiyar cin "cin amanar kasa", zagon kasa a fannin tattalin arziki, da cin zarafin 'yancin kan kasar.

Har yanzu AfriForum ba ta fito ta ce komai ba kan wannan shigar da kara.

A nasa bangaren, Malema ya goya wa Ramaphosa baya kan yadda ya ki baiwa Amurka damar ta zalunci Afirka ta Kudu.

"Amurka ta zalunci kasashe a baya tare da saka takunkumai yadda ta ga dama ba gaira ba dalili kuma tana barazanar yakar kasashe.

"Amma mu jama'a ne da suka bambanta da sauran," in ji shi a zauren majalisa.

"Mun yarda da kai, Shugaban Kasa, cewa bai kamata a zalunce mu ba. Muna zaune a kan kafadun kakanninmu da da suka kalubalanci wannan tsari da rayukansu, kuma mun shirya mu bi sahunsu. Mu ba matsorata ba ne, kuma kar su takale mu," in ji Malema.

Fararen fata a Afirka ta Kudu na zaune a kasar sama da hekaru 300

Umarnin na Trump ya hada da na taimakawa 'yan Afirka ta Kudu farar fata su zauna a Amurka a matsayin masu neman mafaka, don guje wa muzantawa.

Wadannan farar fata 'yan Afirka ta Kudu sun fito daga tsatson 'yan kasar Holland manoma da suka je kasar karni da dama da suka wuce a lokacin mulkin mallaka.

Sun kai yawan kashi 8 na jama'ar Afirka ta Kudu da ke da sama da mutane miliyan 63 kuma na daga cikin wadanda suka fi kowa arziki a kasar.

Sai dai kuma, wadannan farar fata sun nuna kin amincewa da bukatar da Trump ya kima musu na zama a matsayin masu neman mafaka inda suka goyi bayan gwamnatin Afirka ta Kudu.

"Ya kamata ku fahimci Afirka t Kudu kasa ce mi alfahari da kanta, alfahari sosai. ce a mayar da 'yan kasarta zuwa msu neman mafaka, ba na tunanin za su yarda da hakan," Farfesa Monyae ya shaida wa TRT Afrika.

"Magana da gaskiya, duk da wannan surutun da suke yi, rasa Afirka ta Kudu zai zama babban kutufo. Ba za su taba samun rayuwa irin wadda suke samu a nan ba," ya kara fada.

Wakilan fararen fatar Afirka ta Kudu sun ce suna da alaka da kasar da ma nahiyar, kuma sun musanta yin kiran a saka wa Afirka ta Kudu takunkumi.

Da ya sun yi mamakin kiran sauya matsuguni da Trump ya yi, wasu sun nuna bacin rai, yayin da wasu kuma suke wa batun izgilanci a shfukan sada zumunta, suna tambayar ko ma akwai bukatar hakan tun da fari.

Shugaba Cyril Ramaphosa ya kafa gwamnatin hadin kai bayan jam'iyyarsa ta ANC ta rasa rinjaye a majalisar dokoki.

Batun hadin kai a tsakanin 'yan siyasa da kungiyoyin Afirka ta Kudu ba irin wanda aka saba gani ba ne, duba da yadda ba a fi shekara guda ba da gudanar da zaben kasar mai zafin gaske, wanda jam'iyyar ANC mai mulki ta rasa rinjaye a majalisar dokoki a karon farko tun bayan kawo karshen mulkin farar fata tsiraru a 1994.

Wannan koma baya ya tilasta wa ANC kafa gwamnatin hadaka. Duk da irin wannan hadin kai ba shi da yawa, ba dukka ne ke tafi yadda ake so ba.

Jam'iyyar DA, wadda ita ce ta biyu mafi girma a kawancen, ta shigar da kara kotu tana kalubalantar wasu bangarori na dokar kwaskwarima ga tsarin mallakar kasa.

Sai dai kuma, jam'iyyar ba ta nuna goyon baya ga umarnin Trump na dakatar da baiwa kasar Afirka ta Kudu kudi ba, kuma ta yi watsi da ikirarin cewa dokar ta bayar da damar kwaje gonaki - muassamn ma na fararen fatar Afirka ta Kudu.

"Ba gaskiya ba ne cewa Dokar na bayar da dama ga gwamnati ta kwace gonakin yadda ta ga dama, kuma ta tanadi biyan diyya ga duk wadanda aka karbi tasu," in ji DA, wadda tas amu goyon baya mafi yawa daga fararen fata 'yan Afirka ta Kudu.

TRT Afrika