Shaiyene Fritz: 'Yar Afirka ta Kudu da ta zama gwarzuwar duniya a wasan Sunuka

Shaiyene Fritz: 'Yar Afirka ta Kudu da ta zama gwarzuwar duniya a wasan Sunuka

Shaiyene ta zama wata tauraruwa mai haskaka wa a Afirka ta Kudu bayan samu lambobin zinare biyar da azurfa uku.
Shayiene da tawagarta a Gasar Duniya ta 2022 a Moroko. Hoto: Shayiene

Wata 'yar yarinya Afirka ta Kudu wacce ta taso a tsakiyar tashin hankali ta zama gwarzuwa a duniya a wasan da ta ce "ya ceci rayuwarta".

Shaiyene Fritz, mai shekara 22, ta bayar da labarin kuruciyarta tare da 'yan daba a tsaunin Lavender a birnin Cape Town da kuma yadda wasanni suka ceto rayuwarta daga lalacewa.

Shaiyene ta zama wata tauraruwa mai haskaka wa a Afirka ta Kudu bayan samu lambobin zinare biyar da azurfa uku.

"Idan kana yaro karami a tsaunin Lavender Hill za ka ga abubuwa iri-iri wadanda dole ka rayu da su. Ba za ka taba jin dadin kuruciyarka ba kamar yadda sauran yara suke ji," kamar yadda ta shaida wa TRT Afrika.

"Unguwar cibiyar 'yan daba ce, kuma ana yawan samun 'yan mata da suka yi ciki. Tasowa a unguwa da ka saba ganin wadannan abubuwa, yana da wahala ka zama wani abu," in ji ta.

Wannan yana nuna yadda Shaiyene ta yi tsayuwar daka kuma ba ta bari munanan ayyukan da ake yi a unguwarsu sun yi tasiri a kanta ba.

Dalibalar wacce take shekara ta uku a Jami'ar Stellenbosch, ta ce tana tuna lokacin da take shekara tara, saboda an kori mahaifiyarta daga aiki sun bar flat mai daki uku zuwa mai daki daya a tsaunin Lavender Hill.

Daga nan ne sai wani abu mara dadi ya faru. 'Yan daba sun caka wa yayan Shaiyene wuka a shekarar 2018, inda aka kwantar da shi a asibiti har tsawon wata daya.

"Yayana ya yi hatsaniya da wani da yake da alaka da 'yan dabar unguwar. 'Yan daban sun so su kashe shi saboda haka," in ji ta.

"Idan ka taso a irin wannan unguwa kana bakin kokarinka ka ga ka nisanta kanka daga wadannan 'yan daban.

A wani lokaci kwatsam ba ka gani ba, ba ka gani ba, sai matsala ta hada ka da su." A matsayinta na dalibar kwaleji, Shaiyene ta taba doje wa harsashi yayin da take hanyar koma wa gida daga makaranta wata rana.

"Haka kaiwa sai aka fara harbe-harbe, wannan ya sa muka tsere zuwa wani gida har sai bayan da muka daina jin harbe-harben. Idan a tsaunin Lavender Hill ka girma, za ka saba da jin irin wadannan abubuwa.

Za ka rika jin harbe-harbe a kodayaushe, hatta yayin da kake kwance a kan gado kuma ana harba harsashi a gidaje da ba su da nisa da mu. Mutane sun saba da jin haka," in ji ta.

Karamar Gasa

Tasowarta a cikin tashe-tashen hankula, ta zabi ta rika zuwa wurin da ake buga wasan Sunuka a kantunan tsaunin Lavender Hill.

Tana zama ne a can idan ba ta komai, ta fara sha'awar wasan ne lokacin da take da shekara tara da haihuwa daga nan kuma ta koma wasan Sunuka kacokan.

Zagaye goma na wasan tana bukatar ta biya Rand 10 (dala 0.50) kuma ba ta da-na-sanin kashe kudinta a wasan.

"Mun fara wasa tsakanin shagunan Sunuka a unguwar. Muna kiran wasan Lig din sada zumunta kuma kokarin doke maza ne a wasan," in ji Shaiyene.

Shayiene ta fara wasanni tana da shekara 9. Hoto: Shayiene

Yayin da lokaci yake tafiya, kwarewarta tana karuwa ne kuma ta dauki hankalin masu daukar manyan 'yan wasa.

"Na dauke ni domin na je na fafata da wasu shaguna a lig din sada zumunta. Mun yi haka kusan tsawon shekara daya, daga nan ne sai muka fara buga lig din lardi."

A shekarar 2015, Shaiyene da tawagarta sun yi nasara a gasar zakaru ta kasa. Wannan muhimmin lokaci a gareta, kuma daga bisani ta sake lashe wani kofi na tawagar mata.

"A shekarar 2016, mun sake lashe wannan kofi. A wannan shekara ce na fara buga wa tawagar 'yan mata a karon farko. Ni ce mafi karabcin shekaru a cikin tawagar, kuma a karshe mun lashe gasar kofin 'yan mata na 2018," in ji ta.

Jajircewa shi ne wasan

Ina buga wasa a matakin kasa tun shekarar 2015 mataki ne mai wuya kaiwa. Shaiyene ta kan sha wahaya a wasu lokuta wajen samun kudin da za ta je ta yi wasanni.

"Na taba tara dala 526 a shekara don na biya na yi wasa a wasu gasa biyu. Tasowa a gaban mahaifiyata wacce ba ta da aikin yi, ya zama mana wajibi mu nemo kudi," in ji ta.

"Ina kewaye unguwa ina sayar da tikitin caca. Tun daga shekarar 2014 nake tara kudi." Game da babbar gasar da za a yi a kasar Rasha, Shaiyene na bukatar tara dala 160 – abin da ta yi cikin sauki.

Ko da yake akwai lokutan da take zuwa wurin wasa inda da wuya take samun abin da za ta ci.

A bara, ta je birnin Johannesburg daga Cape Town don ta fafata a babbar Gasar Sunuka ta Afirka ta Kudu. Bayan wasan tana da dala 10 ne kacal a aljihunta, ba ta da masani kan yadda za a yi ta koma gida.

Ko da yake kwalliya ta biya kudin sabulu, tun ta samu matsayi na 9 a fanninta, inda ta shiga cikin tawagar da za ta wakilci kasar Afirka ta Kudu a Babbar Gasar Sunuka ta Duniya a Maroko.

"Kowannenmu ya samu Rand 500 a matsayin kyauta, wanda ya isa ya biya min kudin bas na koma wa gida," in ji Shaiyene.

Kungiyar dalibai ta tara mata dala 2,000 da ake bukata a je wata gasa a kasar China a watan Maris din bana.. Photo: Shaiyene 

"Game da tafiya Maroko, sai da na tara kimanin Rand 40,000 (dala 2,100). Na shirya wasan caca da sayar da dambun nama tare da taimakon sarayina. Mun rika sayar shi kowane daya a kan dala 2."

Ko da yake sayar da tikitin caca da dambun naman kawai ba za su samar mana da kudin da muke bukata ba.

Haka kwatsam wani kamfanin Afirka ta Kudu da ya kwashe wajen samar da teburan sunuka ya zabi Shaiyene da ta zama ambasadansa, inda suka ba ta kyautar teburin sunuka wanda ya ba ta damar shirya manyan wasanni.

"Na samu kusan Rand 30,000, wanda shi ne kusan dala 1,500. Wannan abu ne mai kyau tun da wannan ne karon farko da na samu karbuwa wajen wani kamfani.

Ya dauki wata uku da rabi kafin na tara duka kudin, kuma sai hakan ya karfafa min gwiwa don na yi tafiyar," in ji Shaiyene.

Gwarzuwar duniya

Babbar nasarar da Shaiyene ta samu ita ce a Maroko, lokacin da ita da tawagarta suka yi nasarar lashe gasar duniya. "Ina matukar alfahari da kaina bayan na samu lambar zinare. Abu ne da na ji dadinsa sosai," in ji ta.

Yarinyar ta sadaukar da nasararta ga iyalanta da dalibi a Jami'ar Stellenbosch saboda yadda suka ba ta goyon baya a matsayinta na kwararriyar 'yar wasan sunuka.

Kungiyar dalibai ta tara mata dala 2,000 da ake bukata a je wata gasa a kasar China a watan Maris din bana.

"Kawai sai suka fara kawo gudunmuwarsu kuma suka wallafa labarina wanda ya sa na kara samun gudunmuwa.

"Na samu wata babbar gudunmuwa daga wani da ya boye sunansa, wanda ya ba ni Rand 15,000, wato kusan dala 700 kenan," in ji Shaiyene. "Da wannan kudi zan iya sayan tikitin jirgina zuwa China."

Daga dawowarta daga China, Shaiyene da saurayinta sun kafa gidauniyar Shaiyene Fritz Foundation a watan Mayu. Gidauniyar ta mayar da hankali ne a kan bai wa yara damar karatu ta hanyar ba su tallafin kudi da ba su horo.

"Akwai dalibai da dama da suke son zuwa Argentina don buga kwallon kafa ko kuma Ingila don buga wasan Rugby, sai dai iyayensu mata ba za su iya daukar nauyinsu ba," in ji Shaiyene.

"Yana da kyau a taimake su saboda kada su fada kalubalen da na shiga na tara kudi da kaina."

TRT Afrika