Tendani Mulaudzi ta kwashe shekara shida tana tu'ammali da hodar ibilis kafin ta daina sha. Hoto: TENDANI

Wata 'yar jaridar kasar Afirka ta Kudu ta tuna yadda ta yi mugun sabo da shan hodar ibilis (Cocaine) da kuma yadda batun neman agaji yake da matukar muhimmanci wajen kaucewa shaye-shayen.

Daina shaye-shaye ba shi ne kishiyar tsananin sabo da shaye-shaye ba; suna da alaka. A wata lakca ta TED talk wanda ta sosa zuciyar duk wani da ya yi sabo da shaye-shaye kuma yake son dainawa, mai jawabi kuma marubuci dan kasar Birtaniya da kuma Switzerland Johann Hari ya yi bayani kan yadda za mu daina munanan dabi'u wadanda suke son rusa mu.

Darasi ne da 'yar jarida 'yar Afirka ta Kudu, mai shekara 30, Tendani Mulaudzi ta koya cikin wahala, ta kwashe shekara shida tana tu'ammali da hodar ibilis kafin ta daina sha, inda ta tsira da mutuncinta da kuma duk wani abu da ta sanya a gaba.

"Wannan ya faru ne a shekarar 2014, kimanin watanni 11 bayan mahaifina ya rasu sanadin ciwon kansa, kuma daga nan na fara shaye-shaye don danne damuwar rashinsa," kamar yadda Tendani ta shaida wa TRT Afrika.

"Muna zuwa kulob ne mu yi shaye-shaye kafin muka koma gidan wata kawata, inda aka ba ni hodar ibilis," in ji ta.

Abin ya fara ne kamar gwaji lokacin fati da kawayenta kuma daga bisani sai abin ya bi jiki. Tendani wacce a lokacin take shekarar karshe a Jami'ar Cape Town, ta ce ta taba shan miyagun kwayoyi "sau daya a rayuwarta", amma ba ta taba tunanin za ta yi mummunan sabo da hakan ba.

Bayan fara shan hodar ibilis, Tendani wacce ta karanta fannin aikin jarida da shirya fim ta koma cikin hanzari daga wadda ta san kanta zuwa mai cike da kwarin gwiwa. Amma farin cikin da ta samu gajere ne. Da zarar abin ya sake ta, sai ta kara neman kari.

Tendani ta rika kashe kudin inshorar mutuwar mahaifinta wajen sayan kayan shaye-shaye, inda ta kashe kudin gaba daya a cikin shekara daya.

"Lokacin ina shekara 20 kuma ina ji kamar kudin ba za su kare ba, saboda haka daga nan sai abubuwa suka tabarbare min. A shekarar ne na yi watsi da karatun babban digirin da nake a fannin shari'a," in ji ta.

Matsalar ta bazu

Kilo daya na hodar ibilis a Afirka ta Kudu ana sayar da ita ne a kan dala 26,000 zuwa 29,000 a shekarar 2022, kamar yadda rahoton Ofishin Majalisar Dinkin Duniya kan Miyagun Kwayoyi da Laifuka (UNODC).

Ga Tendani ilimi ya taka rawa wajen dawowarta kan hanya, ya taimaka mata wajen fita daga tsananin sabon da ta yi wa shaye-shaye. Hoto: Tendani

Ko da yake haram ne shan hodar ibilis, amma kuma hakan ya bazu a duniya. A gaba daya duniya akwai mutum 350,000 da suke shan hodar ibilis a kullum, kamar yadda bayanai daga hukumar yaki da manyan laifuka tsakanin kasa da kasa ta Global Initiative against Transnational Organised Crime suka bayyana.

Abu mafi muni shi ne Ofishin Majalisar Dinkin Duniya kan Miyagun Kwayoyi da Laifuka (UNODC) ya yi hasashen cewa masu tu'ammali da miyagun kwayoyi za su karu da kaso 40 cikin 100 nan da shekarar 2030.

Ga Tendani ilimi ya taka rawa wajen dawowarta kan hanya, ya taimaka mata wajen fita daga tsananin sabon da ta yi wa shaye-shaye.

Duk da cewa shaye-shayenta ya ta'azzara, ta ci gaba da karatunta a fannin aikin jarida, inda ta kasance cikin dalibai biyar mafiya hazaka a ajinsu a shekarar 2016.

An kori Tendani daga aiki a lokuta da dama saboda tsananin sabo da shaye-shaye, kuma hakan ya shafi alakarta da mutane wanda hakan yake damunta ko bayan da ta daina shaye-shaye.

A shekarar 2017, an ba ta damar gurbin koyon makamar aiki a wani kamfani. Shugabanninta sun fahimci tana da basirar aiki kuma daga nan sai suka kara mata matsayi zuwa mai dauko rahoto.

"Ina iya shirya labarai a cikin minti 30, wanda hakan ya burge su. Saboda na ci gaba da aikin har zuwa shekarar 2018, daga nan ne sai abubuwa suka fara tabarbarewa," in ji ta.

A watan Nuwambar 2018, sai wani shugabanta a wajen aiki ya tambaye ta ko akwai wani abu da take tu'ammali da shi. "Na musanta hakan kodayake suna da bidiyona lokacin da nake aika wa a kawo min barasa kusan kullum."

Saboda tsaninin kunyar da take ji, Tendani ba ta zo aiki ba tsawon kwana biyar, har sai bayan da aka kira ta kuma aka bukaci ta je cibiyar gyara hali.

Mai tsananin shaye-shaye zuwa malama mai gyaran dabi'u

Bayanan da Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) sun nuna cewa kaso 40 zuwa 60 cikin 100 suna koma shaye-shaye kwana 30 bayan barin cibiyoyin gyaran dabi'u, sai kuma wasu kaso 85 cikin 100 da ke komawa ruwa a shekarar farko.

Tendani ba ta san cewa zamanta na wata shida a gidan gyara dabi'u daga baya zai sa ta zama malama a gidan ba.

Tendani ta sake komawa shaye-shaye bayan da ta shiga shirin gyara dabi'u na mako uku a watan Janairun 2019. Daga nan ta koma wani gida na yaki da matsalar shaye-shaye — amma an kore ta daga gidan bayan da aka kama ta tana shaye-shaye.

A Afirka ta Kudu gidajen gyara dabi'u suna aiki tare da kotuna ne wato karkashin dokar Prevention and Treatment of Substance Abuse Act. Hakan ya bisa tilas Tendani ta samu hanyar magance shaye-shayenta na dogon zango.

“Na shafe wata shida a cibiyar gyara dabi'u ta Healing Wings a birnin Nelspruit. Da fari ban so zuwa ba, amma aka ce min idan ban je ba, to za a tura min sammaci daga kotu kuma zan iya yin tsawon shekara daya a can," kamar yadda ta shaida wa TRT Afrika.

Tendani ba ta san cewa zamanta na wata shida a gidan gyara dabi'u daga baya zai sa ta zama malama a gidan ba.

Tendani ta yi aiki a cibiyar Healing Wings ku san tsawon shekara biyu har sai shekarar 2022, lokacin da ta bari don ta fara aiki a fannin sadarwa.. Photo: Tendani

"Na sauya sosai a wata shida kuma daga nan sai na yanke shawarar na tsaya har tsawon wata tara. Daga nan sai na yanke shawarar fara yin aikin sa-kai na tsawon shekara daya kuma daga baya sai na zama malama."

Ta fara bayar da labarin yadda shawo kan matsalar tsananin sabon da ta yi wa shaye-shaye a rubuce – wanda ya zama magani a gareta da kuma gargadi ga saura. "Na fahimci cewa yana da muhimmanci ka mayar da hankali kan yadda za ka daina shan miyagun kwayoyi," in ji ta.

Tendani ta yi aiki a cibiyar Healing Wings ku san tsawon shekara biyu har sai shekarar 2022, lokacin da ta bari don ta fara aiki a fannin sadarwa.

Kamar yadda Johann Hari yake fadi, ta ce tana da wasu kalaman karfafa gwiwa ga wadanda suka yi wa shaye-shaye tsaninin sabo. "Kasance mai kaimi kuma kada ka ji kunyar neman agaji. Daina shaye-shaye ba abu ba ne mai sauki, amma shi ne abin alherin da na taba yi wa kaina."

TRT Afrika