Daga Pauline Odhiambo
Me za ka yi idan mutumin da kake gani a madubi bai yi kyan da ya dace da shi ba?
Zizipho Soldat, wata 'yar Afirka ta Kudu ce mai kirkirar abubuwan da ake wallafawa a Intanet wacce take rayuwa da wata lalura, kuma ana mata wannan tambaya a kowace rana.
Zizipho tana da cutar da ake kira Phocomelia, wani yanayi da ake haifar yariri da matsala a wasu gabobinsa.
Ita an haife ta ne da tawaya a hannunta na hagu yayin da kafarta ta hagu ba ta kai tsawon ta dama ba.
Sai dai wannan bai hana Zizipho zama mai tallan kayan kawa ba, da kuma fara aikace-aikace a kafafen sada zumunta ba, inda ta sauya yadda ake kallon fannin ado da kwalliya na duniya.
Zizipho tana farin cikin cewa ta kulla yarjejeniya da kamfanoni uku na tallan kayan kawa, amma ta sha wahala kafin burinta ya cika.
Lokacin da take karamar yarinya wadda ta taso da wannan lalura, ta sha wahala wajen fahimtar abin da ya sa mutane suke mata wani irin kallo. Tsangwamar da take biyowa baya ita take kara yi wa abin muni.
"Na san cewa akwai wata matsala da nake da ita. A zahiri ina ganin na bambanta da sauran yara mata, sai dai hakan bai dame ni ba har sai bayan da aka fara kara ta," kamar yadda ta shaida wa TRT Afrika.
"Na fada cikin tsananin damuwa ina da karancin shekaru, na gode wa mutane da suke ganin ba zan iya yin wani abu saboda da lalurar da nake da ita."
Yayin da take makarantar sakandare, Zizipho ta fara shan magungunan tsananin damuwa da kuma zuwa ganin likita akai-akai.
Ta kan samu saukin abin da ta yi rubutu a mujalla, abin da ya sa ta kara kwarewa wajen iya magana da mutane. Sai dai ba ta daina tunanin abubuwa marasa dadi ba.
"Na taba yin tunanin kashe kaina. Na ji kamar ba zan iya ci gaba da rayuwa ba. A zuciyata, akwai tunanin cewa da zarar na kai wasu shekaru, to zan kashe kaina kuma har yanzu ina jin haka," kamar yadda ta bayyana.
Sabuwar rayuwa
Ganin manyan-manyan masu tallan kayan kawa kamar Naomi Campbell tana tafiya ya karfafa wa Zizipho zuciya, daga nan ne ta fara tunanin zama mai tallan kayan kawa.
"Lokacin ina makarantar sakandare na rubuta wasika ga wata mujalla, inda na ce ina son zama mai tallan kayan kawa. Kawayena sun ga wasikar kuma sai suka yi min dariya. Sai suka tambaye ni, ' Ta ina kike son zama mai tallan kayan kawa? Kalle ki!"
Wadannan munanan kalamai sun bata ran Zizipho sosai, sai ba su sa gwiwarta ta yi sanyi ba wajen dukufa don zama abin da ta sanya a gaba.
"Na tambayi Ubangiji, 'Yaya za ta halicci mutum mai kyau sosai da zuciyarsa da kuma martabarsa amma kuma jikinsa ya bambanta?'"
Daga nan ne sai Zizipho ta fara daukar kanta hotuna kuma ta rika wallafa su a shafin sada zumuntarta. Sai kuma ta fara magana kamfanonin tallan kayan kawa, sai kuma wani mutum ya ba kwarin gwiwa.
"Na tara kudi don yin ayyukana kuma na biya mutumin Rand 600, abin da ya kai dala 90, amma sai ya cuce ni ya gudu da kudina. Mazambaci ne. Ya bukace ni da na tura masa da hotunan tsiraicina idan ina son zama mai tallan kayan kawa. Lokacin ina da 17 ban san me zan yi ba."
Zizipho wacce yanzu take shekara 28 take a lokacin abin da ya faru ya kara jefa ta cikin tsananin damuwa fiye da wadda take ciki, ga kuma batun tsangwamar da wariyar da jama'a suke nuna mata.
"Yayin da kake girma za ka fara jin abubuwa kamar 'azabtarwa saboda laifukan iyayenka ko kuma kakanninka'. Wannan abin da na yi fama da shi har sai da na girma na yi nawa binciken kan citar Phocomelia."
Ba Zizipho kadai ke fama da wannan lalura ba
Kamar yadda Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana fiye da 'yan Afirka miliyan 80 ne suke fama da nakasa ciki har da masu matsalar kwakwalwa da jariran da aka haifa da wata matsala da wasu lalurori.
Zizipho ta ce hotunan da take wallafa wa a shafukan sada zumunta wasu ba sa sonsu. Yayin nuna mata wariya yake sa ta jin rashin jin dadi na wani dan lokaci, sai ba ta taba karaya daga burinta na zama mai tallan kayan kawa ba.
"Wasu mutane suna cewa ba ni da dabi'a. Suna mamakin abin da 'yar shekara 16 za ta iya yi, yin hotuna sanye da rigar mama. Amma burina shi ne na zama abin da nake son zama," in ji ta.
Yayin da mabiyan Zizipho a shafin sada zumunta suke karuwa ya karu a shekarun nan, haka zalika kwarin gwiwarta. Ta yi karfin halin kara tuntubar wani kamfanin tallan kayan kawa a shekarar 2020.
"Na ce musu, 'ban ni da duka kabobi hudu, amma zan iya tsayuwa na dauki hoto,' kuma na ce ya kamata su dauke ni aiki. Na ce musu ina da irin salo da kwarkwasar da ake so.
Ya za a yi a ce ina da wannan kyau kuma ba za a dauke ni aiki ba? Kwarin gwiwata ya burge ni kuma sai suka dauke ni aiki. Wani kamfani da ke zaune a Birtaniya ya dauke ni aiki bayan ya ga hotuna."
A Birtaniya, bayanan da Majalisar Wakilan kasar ta tattara ya nuna cewa akwai mutum miliyan 14 da ke da nakasa, amma kaso 0.02 cikin 100 na kamfanonin tallan kayan kawa ne suke sanya masu tallan kawa masu nakasa.
Duk da wannan kididdiga, Zizipho tana da kwarin gwiwar cewa adadin masu tallan kayan kawa masu lalura zai karu saboda ci gaba da kiraye-kirayen daina nuna wariya da bukatar da shigo da mabambantan mutane a fannin ado da kwalliya.
Kasar Afirka ta Kudu ta yi amannar cewa damawa da mutane masu lalura a fannoni daban-daban yana da muhimmanci sosai wajen dakile matsalar tsananin damuwa da matsalar masu kashe kansu a tsakanin tsirarun masu fama da nakasa.
"A bara, kawata wacce take da nakasa ta mutu. Ta kasa jure wa kalubalen da ke tattare da rayuwa da nakasa, sai ta zabi ta kawo karshen rayuwarta," in ji Zizipho.
"A ranar da ta mutu, ta wallafa wani hoto kan WhatsApp status dinta inda ta ce tana cikin damuwa. Na so na kira ta don na tambayeta halin da take ciki, amma sai na ce bari na bari sai anjima.
"Na ji haushin kaina na rashin kiranta a kan lokaci, kuma na yi amannar cewa idan da a ce ba ta da nakasa ba za ta kashe kanta ba."
Mutuwar kawarta ya sa sake jefa Zizipho cikin tsananin damuwa, ita kanta ta yi tunanin kashe kanta. Asibitin da take zuwa ne tun tana yarinya ya taimaka mata wajen jurewa da hakuri bayan mutuwar kawarta.
"A wajena tsananin damuwa wani abu ne da mutum yake sabawa da shi sosai, Saboda ina zuwa wajen likita ne shi ya sa na tsira," in ji ta.
Zizipho ta ce ta saba da karbar matsayi na "mai dauke da nakasa" a fannin ado da kwalliya.
"Matsayi 'yan kalilan ne aka warewa mutane irina. Kamfanin da na farawa aiki ya kan sanya ni a matsayi na mutane da ke dauke da nakasa," in ji ta.
"Ina so a sani a kowane irin matsayi kuma sai na ce, "Ka ce kana son mace da take da shekara 20, ko 20 da wani abu mai gashi da yawa? Ni ce irin wacce kuke nema. Ina da jiki ne kawai da ya fita daban.'"
Ta ce kafar sada zumunta tana da rawar da za ta taka wajen gyara yadda ake kallon mutanen da ke dauke da wata nakasa. Bayan kafafen sada zumunta, ta inganta rubuce-rubuce da wallafa abubuwa da take yi wadanda suka shafi rayuwa da nakasa a shafukan intanet.
"Ina ba mutane irina kwarin gwiwa kan su koyi wani abu dangane da rubuce-rubuce da za a sansu da shi," in ji Zizipho wacce ta karanta fannin hulda da jama'a da kimiyyar sadarwa a Jami'ar Walter Sisulu University a birnin Mthatha a kasar Afirka ta Kudu.
Kuma ta taba yin mai bayar da umarni a fim kan nakasa. Zizipho ta ce tana da burin shiga manyan tallace-tallacen kayan kawa da ake yi biranen New York da Paris, da kuma burin rubuta littafi da fara yin kayan kwalliya da zai dace da masu nakasa.
"Ina so na kirkiro wani kayan kwalliya na kowa da kowa, amma wadda zai dace da kowa. Misali jan baki, ka yi tunanin wacce ba ta hannu kuma tana so ta shafa jan baki. Ina so na kirkiri kayan kwalliya wanda masu nakasa za su iya shafawa cikin sauki."