Dan Zimbabwe Siyayi Chinemhute, wanda yake zaune tare da iyalansa a Afirka ta Kudu bisa ka'ida. Hoto: Reuters

Daga

Takunda Mandura

Patricia Marima, wata uwa ce 'yar Zimbabwe wacce take rayuwa a garin Benoni da ke kusa da birnin Johannesburg a Afirka ta Kudu tun shekarar 2008, ta yi farin ciki bayan da ta fahimci cewa tana da har zuwa watan Disamba don gyara takardunta na zama a kasar bisa ka'ida.

Kamar sauran 'yan uwanta 'yan Zimbabwe da ke zaune a Afirka ta Kudu, Marima ta ji sauki a ranta bayan da Ministan Harkokin Cikin Gidan kasar Dokta Pakishe Aaron Motsoaledi ya fitar da wata sanarwa kan baki a makon jiya.

Sabon umarnin da ya bayar ya bai wa 'yan Zimbabwea kimanin 178,000, wadanda suka shiga kasar ba bisa ka'ida ba kuma ake shirin tasa keyarsu zuwa gida, damar zuwa karshen watan Yuni su nemi izinin ci gaba da zama a kasar.

"Dage wa'adin ba abu ba ne da nake tsammani, ban zata ba, abin da ya sa na ce haka kuwa shi ne saboda an taba dagawa sau biyu a baya, yanzu kuma shi ne karo na uku," kamar yadda Patricia Marima ta shaida wa TRT Afrika.

''Ina da kwarin gwiwa za mu gama komai kafin watan Disamba. Ina so na ci gaba da kasancewa a nan saboda 'ya'yana hudu, rayuwarsu tana nan ne," in ji ta.

Tsarin da ya bai wa 'yan Zimbabwe damar zama a nan da yin aiki da kuma karatu zai zo karshe a ranar 30 ga watan Yuni, abin da ya bar su da zabi biyu ko su sake neman wata visar ko kuma su koma Zimbabwe.

Akwai kimanin 'yan Zimbabwe 773,000 da ke zaune a Afirka ta Kudu wadanda suke neman ayyuka, kamar yadda hukumar kididdiga ta Zimbabwe ta bayyana.

Akwai 'yan Zimbabwe 178,000 masu rike da shaida zama da yin aiki (ZEP) na wucin gadi a Afirka ta Kudu.

An kirkiro shirin ZEP bayan da gwamnatin Afirka ta Kudu ta daga wa 'yan Zimbabwe kafa wadanda suka shigo kasar ba bisa ka'ida ba, yawancinsu sun tsere wa matsalolin tattalin arziki da siyasa a kasarsu.

Yawancin 'yan Zimbabwe da suka amfana da shirin ZEP sun shigo kasar ne fiye da shekara 10 da suka wuce. Hoto: Reuters.

Gwamnatin Afirka ta Kudu ta canja shirin Special Dispensation for Zimbabweans da Zimbabwean Special Permits (ZSP) a 2014, sai kuma ta kara canjawa a shekarar 2017 inda ta bullo da shirin ZEP.

“Muna karbar bukatun mutane 1,000 zuwa 1,500 a kowace rana," kamar yadda Kafar Yada Labarai ta Afirka ta Kudu ta ruwaito Minista Motsoaledi yana cewa.

Kura-kuren da ake yawan samu

Shugaban al'ummar Zimbabwe a kasar Afirka ta Kudu Ngqabutho Nicholas Mabhena ya ce yana da kwarin gwiwa cewa masu rike da takardar ZEP za su iya sabunta takardunsu a Afirka ta Kudu musamman saboda yadda aka kara wa'adin.

“Wannan kara wa'adin ba karamin muhimmanci yake da shi ba ga rayuwar dubban 'yan Zimbabwe wadanda suke kokarin samun takardun zama kamar yadda aka bukata daga umarnin gwamnati ta fitar a ranar 25 ga watan Nuwamban 2021," kamar yadda ya shaida wa TRT Afrika.

Kamfanin da yake aikin bayar da bisa (VFS) ya bude wasu karin ofisoshi don a rage yawan lokacin jira.

"Mun bukace su taimaka wa wadanda suka neman takardunsu. Kuma mun nemi su kara adadin wadanda shafinsu na intanet zai iya dauka a lokaci guda kuma su rika duba koke da kura-kuran da masu neman takardu suka yi da sauran matsaloli da za a iya fuskanta a lokacin neman takarda.

"Muna fatan za a samarwa masu neman takardar sauki," in ji Mabhena.

Shugaban Kungiyar 'yan Zimbabwe a ketare Gabriel Shumba ya ce yana da kwarin gwiwa cewa za a samu sauki daga kotuna duk da cewa an dauki mataki a matakin ma'aikata a siyance.

"Muna kira da masu rike da ZEP su canja zuwa wata bisa ta dindindin duk da kalubalen da ake fuskanta," in ji shi.

Kafin kara wa'adi, Zimbabwea ta shirya tsaf don ta taimakawa duk wani da yqke son komawa gida yayin da takardunsu suka kare.

Akalla akwai 'yan Zimbabwe 8,000 da suka yi rijista a cikin zangon farko na masu komawa gida.

Taimaka wa tattalin arziki

Hukumar tattara kudin shiga ta Zimbabwe ta tanadar wa 'yan Zimbabwe wadanda suke son koma wurin da za a ajiye su kuma za su iya tura kayansu gida kafin ranar karewar wa'adin takardunsu.

Akwai dubban 'yan Zimbabwe a Afirka ta Kudu. Hoto: Reuters

Darajar kudin Zimbabwe ya fadi, hakan ya jawo farashin kayayyaki ya lunka idan aka kwatanta da makonni da suka gabata, wannan ya neman zama kalubale ga gwamnatin Shugaba Emmerson Mnangagwa gabanin manyan zabukan da za a yi a kasar a bana.

Kasar da daya daga cikin kasashen da suka fi samar da abinci a nahiyar Afirka – abin da ya sa ake mata lakabi da Bread Basket of Afirka – ta fuskanci gagarumin koma baya a farkon shekarun 2000.

Matsalar da kasar ta fada ta yi mummunar tasiri ga yankin saboda Zimbabwe tana tsakiyar yankin kudancin Afirka, kamar yadda tsohon Shugaban Mozambique Joachim Chissano ya taba cewa.

Ya bayana haka ne lokacin wani taro kan bashi (Structured Dialogue Platform Meeting). An kasa samun bunkasar a shekaru 10 da suka wuce, an rika samun hauhawan farashin kayayyaki da farashin musayar kudin kasashen ketare iri daban-daban da yadda basuka suke karuwa.

Duka wadannan sun kara jawo tsadar tafiyar masana'antu da rage yawan masu zuba jari da sauransu.

'Yan Zimbabwe da suke ketare suna taka muhimmiyar rawa wajen taimaka 'yan uwa da abokan arziki da ke gida ta hanyar kudin da suke aikawa gida.

Baki mazauna Afirka ta Kudu da Birtaniya sun aika da jumullar tsakanin dala biliyan 1.66 zuwa 1.43 a shekarar 2021 zuwa Zimbabwe, kamar yadda alkaluma suka nuna.

Cikin dala biliyan 1.66 dala da aka aika Zimbabwe a bara, kaso 40 cikin 100 (kimanin dala miliyan 583 kenan) na kudin daga Afirka ta Kudu aka aika, yayin da Birtaniya ta samar da kaso 25 cikin 100 (dala miliyan 362).

Kalubalen da ke gaba

"Muna ganin wasu abubuwa da jawo kungiyoyin kin jinin baki a yayinda tattqlin arzikin kasar ya fara murmure daga annobar korona – tattalin arzikin da ke fama da matslar wutar lantarki wanda hakan ya shafi masana'antu," in ji Gibson Nyikadzino, wani mai sharhi kan harkokin siyasa a birnin Harare a kasar Zimbabwe.

'Yan Zimbabwe da ke zaune a Afirka ta Kudu sun dade a cikin halin rashin tabbas. Hoto: Reuters

Gorden Dzikiti, wani dan Zimbabwe ne mazaunin Afirka ta Kudu, wanda yake ganin cewa lokacin da aka ba 'yan uwansa 'yan Zimbabwe don su nemi takardar zama ya yi kadan.

“Lokacin ya yi kadan kowa ya iya kammala, kuma lokaci bai wadaci wadanda aka dagawa kafa ba. Ko ta yaya ka kalli abin ko bayan an daga maka kafa to kana bukatar samun takardar izinin yin aiki.

"Idan na kai takardar izini zuwa ga ma'aikatar harkokin cikin gida, ina bukatar akalla wata takwas kafin ma'aikatar ta kammala aiki a kan takardun," kamar yadda ya yi bayani.

Wata kungiyar lauyoyi da ke yaki da kin jinin baki da kare hare hakkin dan Adam ta Global South Against Xenophobia and Lawyers for Human Rights ta ce soke takardar ZEP ya jawo babbar damuwa kuma rashin adalci ne.

Lauyan kungiyar masu rike da takarda ta Zimbabwe Permit Holders Association Simba Chitando, wanda yake kare kungiyar a shari'ar da take da ma'aikatar harkokin cikin gida a Babban Kotu a birnin Pretoria, ya ce kara wa'adin ya kawo wa masu rike da takarda ne sauki na wucin gadi.

"Abin da ya fi shi ne kawai samun takardar izinin zama ta dindindin," in ji shi. Bankuna sun fara aika wa da sakonni cewa za su rufe asusun ajiyar masu rike da takardar ZEP ta wucin gadin a ranar 31 ga watan Disambar 2023 – abin da yake kara sanya tsoro a zukata.

TRT Afrika