Daga Sylvia Chebet
Shugaban lardin Gauteng na Afirka ta Kudu, wanda Johannesburg ne babban birnin yankin, ya yi kira ga mazauna wajen da bankuna da masu sana'ar sayar da kayayyaki da su koma tsarin takaita ta'ammali da tsabar kudi don rage yawaitar fashi da makamin da ake fuskanta.
Shugaban lardin Panyaza Lesufi ya yi amanna da cewa saye da sayarwa ta intanet ko katin banki, zai taimaka wajen hana ɓarayi yin sata.
Lesufi ya sanar ta shafinsa na X cewa "Idan muka rage amfani da tsabar kudi a lardinmu, wannan haukan na fashi a makami zai kau."
Ya kara da cewa "Ya zama dole shagunan da ke sayar da kayayyaki su yi aiki da wannan kira namu na daina karbar tsabar kudi."
Jama'a na tantama
Wannan abu da Lesufi ya rubuta a shafin sada zumunta ya janyo mayar da martani inda wasu suke tantama kan tasirin wannan yunkuri.
Da yake yaba wa karfin ta'ammali da yanar gizo a Gauteng, shugaban lardin ya kuma ce "Mu lardi ne da ya kware wajen ta'ammali da hada-hadar zamani. Ko tsofaffi idan sun tambayi a ba su kudi sai su ce ga 'EWallet' ka turo min."
Ya kuma ci gaba da cewa "Idan ba ka da tsabar kudi da yawa, ba za a samu fasa cibiyoyin bayar da kudi ba, idan ba tsabar kudi, ba wanda zai fada hali irin wannan, idan ba ka da tsabar kudi, ba za a yi maka fashi ba."
Akwai damuwa kuma kan cewa za a yi wa wasu nisa a fannin tattalin arziki a Gauteng, saboda tattalin arziki Afirka ta Kudu na ta'ammali da kudade sosai.
Har yanzu ana ne sa da aiwatar da wannan shiri, in ji Aluwani Chokoe, shugaban watan kungiyar harkokin sadarwar yanar gizo da suka mayar da hankali wajen inganta fasahar ta'ammali da kudade a zamanance.
Chokoe ya kawo misalin yadda intanet ke fuskantar kalubale wajen amfani ga daidaikun mutane, kasuwanci da a ofisoshin gwamnati irin su asibiti wadanda suke hidimtawa jama'a kullum.
Ya fada wa TRT Afirka cewa "Muna bukatar kayan sadarwar yanar gizo saboda kasuwancin zamani yadda a kalla mafi yawan jama'ar Afika ta Kudu za su samu damar kasuwancin a saukake."
Wani mai tantama kan wannan batu a shafin X mai sunan @TMbuzi ya ce "ba zai yiwu a daina ta'ammali da tsabar kudi baki daya ba a wannan yanayin da ake ciki. mafi yawan jama'armu sun dogara ne ga bangarorin da ba na hukuma ba don rayuwa."
Mai amfani da shafin sada zumunta din ya bayar da shawara ga gwamnati da ta "magance wannan matsala ta fasi da makami ta hanyar samar da jami'an 'yan sanda."
Chokoe ya kuma yi nuni da cewa akwai bukatar karfafa tsaron intanet da dokoki kamar yadda jami'an tsaron za su iya sanya wa a koma barna ta yanar gizo.
Ya ce "Muna bukatar tsauraran matakai don magance matsalar satar bayanan mutum da karya ka'idar amfani da bayanan."
Tuni 'yan sanda suka kaddamar da farautar 'yan fashin da suka yi awon gaba da wasu makudan kudade da ba a bayyana ko nawa ba ne a wata motar a kori kura a babbar hanyar kudancin Johannesburg.
Makoma da babu tsabar kudi
Kasashe, kasuwanci da mutane sun koyi darussa kan muhimmancin takaita ta'ammali da tsabar kudi a lokacin annobar korona, inda mutane suka koma amfani da kati wajen biyan kudade saboda hana fita da kusantar juna da aka yi.
A Afirka ta Kudu, amincewa da amfani da tsarin biyan kudade ta fasahar zamani inda Fintech yake ta kara habaka tare da kamfanunnuka da kungiyoyi inda suke samun fasaha maimkyau wajen aika kudade.
Sai dai kuma, sha'anin tattalin arzikin Afirka ta Kudu a tsakanin jama'a gama-gari ya dogara kan tsabar kudi da ke kai komo.
Kiran da Lesufi ya yi kan a koma ta'ammali da kudade ta yanar gizo da katin banki, na iya zama bayar da shawara kawai, sama da asalin kiran a kawar da amfani da tsabar kudin.