Duniya
Me ya sa yara 'yan ƙasa da shekaru 20 a Ingila suka fi kowa rashin farin ciki a Turai?
Abin da ake kira "rushewar farin ciki", sama da kashi daya cikin hudu na matasa 'yan kasa da shekaru 20 a Birtaniya sun bayyana a cikin rahoton rashin samun gamsuwar rayuwa cewa hauhawar farashi da tsadar rayuwa ne ummul'aba'isin jefa su a yanayin.Kasuwanci
Afirka ta Kudu za ta fito da tsarin biyan tara don haɓaka ayyukan yi ga baƙaƙen fata
Dokar samar wa baƙaƙen fata ayyukan yi ta shekarar 2003 ta ƙarfafa gwaiwar kamfanoni su ringa ɗaukar baƙaƙen fata aiki tare da ƙara musu girma ta hanyar sassauta musu haraji da kuma damar samun ƙwangilolin gwamnati.Karin Haske
Eco-jogging: Yadda matasan Benin ke tsaftace wuraren taruwar jama'a.
Wani gangamin tsaftace muhalli da ya ƙunshi masu tattakin motsa jiki, waɗanda ke tsince ledoji da sauran shara a kan hanyarsu, ya sauya abin da ya fara a matsayin wani abin sha'awar wani ɗalibin jami'ar Benin zuwa wata kungiyar kawo sauyi.Afirka
Matasan Ghana miliyan 1.9 ba su samu ilimi ko aiki ko wani horo ba - Rahoto
Binciken, wanda Hukumar Ƙididdiga ta Ghana ta fitar, ya yi nuni da cewa mata ne suke da adadi mafi yawa na mutum miliyan 1.2 yayin da maza ke da adadin 715,691 a cikin matasan Ghana da ba su samu ilimi ko aiki ko kuma wani horo ba.Duniya
Nijeriya na cikin ƙasashen da yawan al'ummarta zai yi ta ƙaruwa – MDD
Yawan haihuwa a duniya ya kai 2.3 a kowace mace, kuma yawan tsofaffi na karuwa a sassan Turai da Arewacin Amurka da Asiya. Ana sa ran a 2074 yawan mutane ‘yan shekara 65 zuwa sama zai kai 20.7%, sannan yawan ‘yan shekara 80 zuwa sama zai ƙaru sau ukuRa’ayi
Shin nasarorin 'yan wasan Afirka a duniya na nufin wasan na samun ci gaba a nahiyar?
Bambancin da ke tsakanin kwallon kafa na Afirka da na Turai na zama dalilan da yawancin matasa 'yan wasan Afirka suke daukar matakan guje wa rashin tabbas da suke tsintar kansu a kasashensu, ba tare da la'akari da samun nasara ko akasin haka ba.Afirka
Magance rashin aikin yi a matsayin mabudin ci gaban tattalin arzikin Afirka
A Afirka, inda sama da kashi 60 cikin 100 na al'ummar yankin matasa ne 'yan kasa da shekaru 35, magance wannan matsala ba wai kawai a matsayin al'amari da ya shafi zamantakewa bace amma a matsayin wani muhimmin fanni na tattalin arziki da ake bukata.
Shahararru
Mashahuran makaloli