Mutanen kabilar Ndau suna da yawa a Gabashin Zimbabwe, sannan sun fi mayar da hankali a fannin noma.      

Daga

Charles Mgbolu

Mutanen kabilar Ndau suna da yawa a Gabashin Zimbabwe, sannan sun fi mayar da hankali a fannin noma.

Cikin ikon Allah kuma, sunan garinsu din Ndau na nufin kasar noma, hakan ya sa girbe kasa domin samun abinci ya kasance cikin al'adun mutanen yankin tun shekaru aru.

Sai dai UNESCO na gargadin cewa amfani da dabarun noma na zamani sun fara maye gurbin na dauri domin samun yabanya mai kyau da yawa saboda karuwar bukatar abincin a kasuwa.

"Duba da fargabar samun karancin ruwan sama da kusan kashi 30 a shekara 10 masu zuwa saboda sauyin yanayi, manoma sun fara nemo hanyoyin da za su kaucewa wannan barazanar da ke fuskanto su," kamar yadda rahoton UNESCO ya bayyana.

Mutanen yankin suna yaba wa kokarin Philip Kusasa, wanda malami ne a Chikore High School da ke Chipinge, a yankin Kudu maso Gabashin Zimbabwe, wanda kuma shi ne ya assasa Taron Fasahar Ndu wato Ndau Festival of Arts domin wayar da kan mutane muhimmancin adana al'adunsu na noma da ya fara bacewa.

Ana koyar da manoma hanyoyin noma kayayyakin lambu. Hoto: UNESCO

Taron ya kuma samar da wata damar ta wayar da kananan manoman yankin, wadanda yawanci mata ne, dabarun noma da tallafa musu.

Haka kuma bayan harkokin da suka shafi noma a taron, a gefe guda kuma ana rakashewa da kade-kade da raye-raye na al'adun mutanen yankin.

Babban abin ban sha'awa a wajen taron kuma shi ne horon da manyan manoma suke ba matasan manoma a kan yadda za su noma kayayyakin lambu irin su “Mutikiti” and "Muchicha,” wadanda na'ukan kabewa ne na yankin.

Kusasa bai tsaya a kan ilimantar da manoma ba, yana kuma kokari wajen ganin an koyar da matasan manoman yankin hanyoyin adana kayan nomansu.

An kuma gudanar da kade-kade da raye-raye a wajen taron. Hoto: Ndua Festival/Facebook

Ayyukansa a makarantar firamaren Gaza, na daya daga cikin makaranta 24 a kasashen Namibia da Zimbabwe da yake kokarin ganin sun shigar da koyar da dabarun noma cikin darususansu, na samun yabo.

"Al'adunmu su ne abin alfaharimmu, idan ba mu adana su ba, za su bace," in ji Kusasa.

Daga cikin kokarin da yake yi akwai bukatar makarantun su sanya koyon dabarun noma a cikin tsarinsu, wanda zai saukaka wa shugabanni da malaman makarantun hanyoyin da za su sanya noma a cikin tsare-tsarensu.

Philips Kusasa na shan yabo a cikin da wajen kasarsa. Hoto: Philips Kusasa

"Muna shirin assasa lambun kayayyakin lambunmu na gado, wadand da su za a rika amfani a matsayin abinci a makarantun.

"Daliban za su koyi dabarun noma na dauri da kuma sanin amfani kayayyakin lambu a cikin dan Adam. Daga baya sai lambun ya zama wajen da za a rika amfani da shi wajen koyar da fasahohi da dabarun noma na zamani," in ji shi.

TRT Afrika