Daga Mohamed Guleid
Yayin da yanayin tattalin arzikin duniya ke ci gaba da samun sauye-sauye cikin sauri, daya daga cikin manyan kalubalen da kasashe ke fuskanta, musamman a nahiyar Afirka, shi ne matsalar rashin aikin yi da matasa ke fama da su.
Wannan kalubalen na dada kamari sakamakon karancin damammakin da ake da su ga matasa don samun ingantacciyar rayuwa.
A Afirka, inda sama da kashi 60 cikin 100 na al'ummar yankin matasa ne 'yan kasa da shekaru 35, magance wannan matsala ba wai kawai a matsayin al'amari da ya shafi zamantakewa bace amma a matsayin wani muhimmin fanni na tattalin arziki da ake bukata.
Ci gaba mai dorewa na nahiyar ya dogara ne wajen amfani da bambace- bambace baiwar dake tsakanin matasan Afirka.
Kadarar Afirka mafi girma
Nahiyar Afirka tana alfahari da yawan al'ummarta matasa a duniya, wadanda kashi 65 cikin 100 suke kasa da shekaru tsakanin 25 zuwa matsakaicin shekaru 19.6, a cewar kididdigar Global Entrepreneurship Monitor.
Ana daukar yawan matasan Afirka a matsayin daya daga cikin manyan kadarori da nahiyar ke da shi, wadanda ke da damar habaka ci gaba da tattalin arziki da kuma kimar nahiyar a idon duniya.
Duk da wannan hange, yawan matasan na zama wani babbar barazana idan ba a samar musu isassun damar yin aiki da kasuwanci ba.
Daya daga cikin manyan cikas din da matasan ke cin karo da shi a harkokinsu na kasuwanci shi ne kalubalen samun jari.
Shingayen dake tsakanin samun kudade
Shamaki na kudi wani al'amari ne mai muhimmanci wanda ke bukatar a shiga tsakani don bude arzikin da ke tattare da karuwar yawan matasan Afirka.
A cikin wannan yanayi na magance rashin ayyukan yi tsakanin matasa a Afirka, rashin jagoranci na zama kan gaba a matsayin babban kalubalen da matasa ke fuskanta.
Kazalika, yalwar albarkatun kasa a Afirka na bayar da wata dama ta musamman ta yin amfani da wadannan kadarorin don amfanin matasa da ma nahiyar baki daya.
Hada masu hazaka da kwararru
Samar da shirye-shirye na jagoranci wadanda za su hada ƙwararru da matasa masu hazaka zai iya cike wannan gibin.
Kuma ba kawai a tsara wadannan shirye- shirye don ba da shawara kan zabin sana'a ba har ma don kara haske game da kalubale da ke kewaye da yanayin kasuwancin Afirka.
Kwararrun masana za su iya ilimantarwa da kuma kara wa matasa basira, tare da taimakawa musu gina hanyoyin inganta kawunansu, wadanda duk suke da muhimmaci wajen samun nasarar su.
Idan aka fadada damar da dimbin albarkatun kasa na Afirka ke bayarwa, akwai damar da za a iya samar da ayyukan yi mai dorewa da kasuwanci ga matasa.
Nahiyar tana da arzikin ma'adanai da filayen noma da kuma hanyoyin samar da makamashi, wanda ke bude hanyoyin kirkire-kirkire da bunkasar tattalin arziki.
Gwamnatoci, tare da hadin gwiwar kamfanoni masu zaman kansu, za su iya samar da shirye-shiryen wadanda za su karfafa gwiwar matasa don bude musu kokfofin sana'o'i a sassa kamar na aikin noma da sabunta makamashi da kuma kula da dorewar albarkatun kasa.
Damarmakin tattalin arziki
Alal misali, haɓaka kasuwancin noma da ayyukan noma mai ɗorewa ba guraben aikin yi kawai za su samar ba. har ma da ba da gudunmawa ga wadatar abinci da haɓakar tattalin arziki.
Hakazalika, saka hannun jari a ayyukan samar da makamashi ba wai kawai magance bukatun makamashi na nahiyar ba ne, har ma da samar da wani dandali ga matasa wajen shiga ayyukan kirkire-kirkire da kare muhalli.
Haka kuma, shirye-shiryen jagoranci na iya dacewa da takamaiman bukatun matasa masu sha'awar sassan da suka shafi sarrafa albarkatun ƙasa.
Don haka, magance rashin jagoranci da samar wa matasa damar samun bayanan da suka dace ta hanyar ba da shawara kan sana’o’i, su ne muhimman abubuwan da ke cikin cikakkiyar dabarar magance matsalar rashin aikin yi ga matasa a Afirka.
Ta hanyar haɗa ƙwararrun masu ba da shawara da matasa masu kishi da kuma yin amfani da albarkatu masu yawa na Afirka, nahiyar za ta iya buɗe sabbin hanyoyin bunƙasa tattalin arziƙi tare da bai wa matasanta damar zama masu samar da ci gaba mai ɗorewa.
Jagoranci da zaɓin sana'o'i da aka sani ba kawai za su amfanar da ɗaiɗaikun mutane ba ne, za su ba da gudunmawa ga gina ƙwararrun ma'aikata masu juriya da kuzari waɗanda ke ciyar da Afirka zuwa kyakkyawar makoma mai haske da wadata.
Koyar da sana’o’i
A wannan gaba, kungiyoyin dake taimakawa wajen fara sana’a, sun zama karfen kafa wajen tabbatar da yanayin koyon sana’o’I a tsakanin al’umma.
Wadannan kungiyoyi da suka hada da na kasuwanci zuwa kiwon kaji, na taka muhimmiyar rawa wajen magance matsaloli da dama da masu kananan sana’o’I ke fuskanta.
Suna bayar da shawarwari masu kyau da koma bayar da horo a bangarori masu muhimmanci kamar dabarun kasuwanci, samar da kayayyakin more rayuwa, dabarun tattala kasuwanci, da uwa uba harkokin sarrafa kudade.
Ta hanyar bayar da yanayi na tallafi da damar amfani da muhimman kayayyaki, wadannan kungiyoyi ko kamfanoni na karfafawa masu sana’o’I da wadanda suka fara wasu ayyuka wajen shawo kan matslolin da suke fara fuskanta a farkon fara sana’iarsu, wanda hakan ke bas u damar mayar da hankali ga habaka kasuwancinsu.
Dadin dadawa, shigar da fasahar sadarwa ta zamani ga wadannan hanyoyi na tallafawa, na bayar da samar da karin damarmakin cigaban kasuwanci da isa ga bangarori da dama.
Gwamnatoci a dukkan yankunan Afirka sun fahimci muhimmancin da kananan sana’o’I suke da shi wajen habaka tattalin arziki da inganta yanayin zamantakewa.
Raina, ilmantarwa da bayar da kudade ga masu sana’o’in da suke da hazaka na da matukar muhimmanci a wannan yunkuri da ake yi.
Ya kamata gwamnatoci su aiwatar da manufofin tallafawa masu sabbin dabarun samar da kayayyaki, bayar da horo da ilmantarwa yadda ya kamata, da kuma samar da jari cikin sauki, wanda hakan zai baiwa kasashen Afirka damar taimakawa matasansu su cimma burikansu. Kadara da barazana burikansu.
Kadara da barazana
A yayin da muke kalubalantar rashin tabbas da raguwar karfin tattalin arziki, ya zama wajibi a lalubo hanyoyin zamani wajen tallafaw amatasa masu sana’o’i.
Hanyoyin da aka saba da sub a za su isar ba wajen magance wadannan kalubale na kasuwanci.
Gwamnatoci, kasuwanni da cibiyoyin sarrafa kudade na bukatar hada kai wajen nemo dabarun da za su bayar da kariya ga matasa masu sana’o’I daga karye wa a nan gaba.
Magance matsalar rashin aikin yi tsakanin matasa a Afirka na bukatar babban kokari da hadin kai.Ta hanyar kallon adadin matasa a matsayin wata babbar kadar da kuma barazana, sannan tare da zuba jari a sana’o’I, gwamnatoci da kasuwanni na iya cimma burin nahiyar na zama mai amfanuwa daga matasanta..
Makomar cigaba mai dorewa na Afirka ya dogara kan iyawar nahiyar wajen amfana da karsashin matasanta wajen yin sana’o’i, wanda hakan zai kawo hazakar kirkira, habakar tattalin arziki, da cigaban jama’a.
Marubuci Mohamed Guleid shi ne tsohon mataimakin gwamnan gundumar Isiolo a Kenya
Togaciya: Ba lallai ra'ayin da marubucin ya bayyana ya zama ya yi daidai da ra'ayi ko manufofin dab'i na TRT Afirka ba.