Shugaban Ghana Nana Akufo-Addo ya ce bashin da kasar za ta karba daga Asusun Bayar da Lamuni na Duniya IMF ba zai fitar da ita nan take daga halin matsin tattalin arzikin da take ciki ba.
Kamfanin dillancin labarai na kasar Ghana ya ambato shugaban kasar yana bayyana hakan a ranar Lahadi da dare a jawabin da ya yi wa 'yan kasar.
Ya ce bashin na dala biliyan uku zai sa abokan kasuwanci da sauran masu zuba jari su kara samun kwarin gwiwa kan tattalin arzikin Ghana.
Shugaban ya ce matakin da ya dauka na zuwa IMF neman wannan kudi mataki ne mai kona rai sakamakon gwamnatinsa ta yi kokari wajen kokarin kawar da sauran basussukan da gwamnatocin baya suka karba daga IMF din.
Shugaba Addo ya kara jaddada cewa annobar korona da kuma yakin Ukraine ne ya kara jefa kasar cikin matsin tattalin arziki.
Duk da cewa Shugaba Addo ya ce ba lallai a samu waraka a kasar nan take ba, amma ya ce za a ci gaba da manyan ayyuka na ababen more rayuwa wadanda aka dade ana yi a fadin kasar.
Shugaban ya bukaci duka jama’ar Ghana su bai wa kasar goyon baya domin aiwatar da tsare-tsare da kudin na IMF da kasar ta samu.
A ranar 17 ga watan Mayun 2023 IMF ya amince da bayar da dala biliyan uku a matsayin lamuni ga Ghana.
Kasar Ghana na daga cikin kasashen Afirka masu fama da hauhawar farashi inda yanzu haka matakin hauhawar farashin kasar ke kan kashi 41.2 cikin 100.
Sa’annan kudin ruwan da bankuna ke karba na bashi yana kan kashi 29.50 cikin 100.