Masu motocin haya a Nijeriya sun bayyana karin kudin mota sakamakon matakin da gwamnatin kasar ta dauka na janye tallafin fetur a kasar.
A ranar Litinin ne sabon shugaban kasar Bola Tinubu ya bayyana cewa "tallafin fetur ya tafi" a yayin da yake shan rantsuwar kama aiki.
Tun daga lokacin aka soma ganin dogayen layukan motoci a gidajen mai sannan farashin kayayyaki suka tashi.
Wani yaron mota mazaunin jihar Legas da ke kudancin kasar ya shaida wa TRT Afrika yadda suka kara kudin mota saboda tsadar da fetur ya yi matuka.
Idowu Kilani Babatunde ya bukaci gwamnati ta sauya ra'ayinta kan batun.
"Ni yaron mota ne kuma a halin da ake ciki yanzu man fetur ya yi tsada. Ana sayar da man a gidajen mai amma mafi sauki shi ne naira 490 a kan lita daya; wasu gidajen man suna sayarwa har naira 600.
Yanzu haka farashin motocin sufuri ya yi sama, a baya muna daukar fasinjoji daga nan Yaba zuwa Ojota naira 200 amma yanzu naira 500 muke karba," in ji yaron motar.
Shi kuwa Duniya Gandirunbola ya ce ya shafe sa'a 12 kan layi domin sayen fetur.
Ya ce talakawa ne ke shan wahalar matakin da gwamnatin ta dauka na cire tallafin.
"Na fito sayen mai da misalin karfe hudu na safe, inda na shafe sa'a 12 ina jiran layi ya iso kaina, sai dai abin takaicin shi ne yadda wasu ke yin kutse suna shiga gidajen mai suna ba da na-goro ana ba su man, da ana bin ka'ida da duk wanda ke kan layi zai samu man, amma jami'an tsaro na kallo ake yin wannan," in ji shi.
Ajayi Adekola wani gurgu ne wanda shi ma ya ce cire tallafin ya jawo cikas ga sana'arsa ta tukin motar haya, sai dai shi ya ce bai ganin laifin sabon Shugaba Bola Tinubu dangane da janye tallafin.
"Ni nakasasshe ne kuma na rungumi sana'ar tuki don ba na son bara, yau kwana uku kenan muna fama da matsalar man fetur, ka ga ni direba ne na karamar mota, ina da iyali amma haka yau na fito na yini a layin mai, ban yi aiki ba, bare na samu na abinci," in ji direban motar.
Ajayi ya ci gaba da cewa "ko da yake ba na dora laifin a kan Shugaba Tinubu saboda ya janye tallafin ne don amfanin talaka, sai dai su 'yan kasuwar man ne suke amfani da wannan dama don su gallaza mana."
Shi ma Mista Elaija direba ne kamar Ajayi wanda ya kwashe tsawon yini yana neman man kuma shi ma dora laifin a kan 'yan kasuwa.
"Ni direba ne amma na samu fetur da dan karan tsada. Sai dai a ganina ba laifin shugabaninmu ba ne, laifin na wasu ne da ke cikinmu, saboda 'yan kasuwar sun daina sayar da mai nan take bayan da Shugaba Tinubu ya ba da sanarwar janye tallafin man.
"Bayan a wannan lokacin suna da man a wadace amma sai suka ki sayarwa, don haka ya kamata gwamnati ta dauki mataki, kayyade farashi a ko'ina a kasa, domin yanzu wasu har naira 700 suke sayar da litar man," in ji Mista Elaija.
Shi Mista Victor ya yi tafiya mai nisa ne don ya samu man a farashi mai rangwame.
"Daga can uwa duniya nazo nan sayen man fetur domin nan suna sayarwa naira 418, a unguwarmu kuwa naira 500 ne lita, a wasu wuraren ya kai naira 700 lita daya, fatanmu shi ne a yi wa Allah a dubi halin da talakawa suke ciki," in ji shi.
A nasa bangaren, Mista Ibukun ya nuna goyon bayansa ne ga gwamnati dangane da janye tallafin.
"Ina goyon bayan gwamnati kan janye tallafin man domin mataki ne mai kyau, domin wasu mutane kalilan ne ke amfana da tallafin.
"Don haka wanna kudin da ake kashewa a tallafin mai ya kamata gwamnati ta yi amfani da su wajen inganta kiwon lafiya, hanyoyi da kyautata ilimin 'ya'yanmu, ta kuma yi amfani da kudin wajeninganta harkokin sufuri."
Ya ce a shirye yake ya ajiye motar a gida, idan gwamnatin za ta samar da motocin haya.
"Muddin gwamnatin ta samar da motocin haya, mu alu'ammar gari za mu ajiye namu motocin a gida, kuma hakan zai kawo raguwar cunkoso a gari, ya kuma inganta muhalli, wannan matsala da ake ciki ta dan lokaci ce, na tabbata komai zai zama labari."