Kamfanin mai na NNPCL ya tabbatar da sauya farashin fetur a Nijeriya

Kamfanin mai na NNPCL ya tabbatar da sauya farashin fetur a Nijeriya

Kamfanin ya sanar da sauyin a wata sanarwa da ya fitar a ranar Laraba
Ana samun dogayen layi a biranen Nijeriya sakamakon fargabar cire tallafin man fetur. Hoto/Reuters

Kamfanin man fetur na Nijeriya NNPCL ya tabbatar da samun sauyi a farashin man fetur a hukumance. Kamfanin ya bayyana haka ne a wani sako da ya wallafa a shafinsa na Twitter.

“NNPC Limited na son bayyana wa kwastamominmu cewa mun yi sauyi kan farashin man fetur dinmu a duka wuraren sayar da mai, daidai da yadda yanayin kasuwa yake,” in ji sanarwar kamfanin.

Tun da farko 'yan Nijeriya sun fada cikin rashin tabbas kan hakikanin farashin man fetur tun bayan da shugaban kasar Bola Tinubu ya bayyana cewa "tallafin fetur ya tafi”.

Ya bayyana haka ne yayin da yake shan rantsuwar kama aiki ranar Litinin, sai dai kamfanin man fetur na kasar ya bukaci kada mutane su ji tsoro saboda akwai isasshen mai.

Tun bayan kalaman nasa, aka soma ganin dogayen layuka a gidajen man fetur a fadin kasar.

Maganar Shugaba Tinubu ta zo a dunkule kuma a hukumance ba ta warware cewa ko daga yaushe tallafin zai daina aiki ba.

Bayanai sun nuna cewa a halin yanzu ana sayar da man fetur a farashi daban-daban a jihohin kasar.

TRT Afirka ta tattauna da wasu kan batun inda suka nuna cewa yanzu babu tabbas kan farashin fetur a kasar.

Wani mazaunin birni Kano, Rufai Jega, ya shaida mana cewa ana sayar da kowace lita ta fetur a kan N530 zuwa N550.

Shi kuwa Abubakar Ibrahim da ke zaune a Kaduna ya ce suna sayen lita a kan N450.

A unguwar Ikoyi da ke birnin Legas, ana sayar da man fetur a kan N488 zuwa N500.

Kafafen watsa labarai na kasar na ruwaito cewa an samu matukar kari a kudin sufuri.

A ranar Talata shugaban kamfanin NNPCL ya bayyana cewa bai kamata masu motoci su yi ta sauri-sauri suna sayen mai ba domin akwai isasshe.

Sai dai kungiyar kwadago ta kasar ta sha alwashin bijire wa gwamnatin kan wannan mataki.

Gwamnatin Tinubu ta yi bayani daga baya cewa babu tallafin fetur a cikin kasafin kudin Nijeriya daga watan Yuni inda ta zargi kafafen watsa labarai da juya zance.

“Tinubu ya gaji gwamnati wadda ba ta tanadi tallafin man fetur ba zuwa Yunin 2023,” a cewar Festus Keyamo, wani babban jami'i a lokacin yakin neman zaben na Tinubu.

Gwamnatoci daban-daban sun shafe shekaru suna cewa za su cire tallafin man fetur a Nijeriya sai dai lamarin ya gagara.

An taba kokarin cire tallafin a zamanin Goodluck Jonathan amma zanga-zanga ta biyo baya inda daga baya lamarin ya bi ruwa.

Sai dai a lokacin yakin neman zaben 2023, duka manyan ‘yan takarar shugaban kasa duk sai da suka yi alkwarin cire tallafin man fetur din inda suka ce ba ya da wani amfani.

TRT Afrika