A baya, Kongo na samar da sama da tan 500,000 na gahawa a duk shekara amma a yanzu tan 10,000 take samarwa. Hoto/ La Kinoise

Daga Kudra Maliro

Tysia Mukuna tana daukar kanta a matsayin jarumar gahawa – da tana da dama, za ta “tilasta” yin doka kan shan gahawar Kongo a duk safiya.

A shekara 30, wannan matashiyar, tana da kamfani na cikin gida mai suna “La Kinoise” wanda yake samarwa da sayar da gahawa na kusan shekara uku. “Ina son noma tun ina ‘yan karama; La Kinoise ya hadu da soyayyar da nake wa noma da fikirar da nake da ita kan kasuwanci da kuma ilimina,” kamar yadda Tysia ta shaida wa TRT Afrika.

Gonar kamfanin da ke Kinshasa tana samar da iri na gahawa wanda ake sarrafa shi a La Kinoise kafin kai shi kasuwa.

Tun a watan Afrilu, da wuya mutum ya wuce bai ga amalanke na musamman wanda shago ne na tafi-da-gidanka da aka yi wa fentin kamfanin La Kinoise a kan titi ba.

Akwai kamfanin a wasu birane da suka hada da Lubumbashi da Boma da Matadi.

A halin yanzu amalanken sayar da gahawa na La Kinoise ya samar da aiki ga sama da mutum 200 inda yake ba su dama kusan su ci gashin kansu.

Tysia Mukuna da ma'aikatanta na aiki kan irin gahawa. Hoto/La Kinoise

Zuwa 2024, kamfanin na da burin daukar gomman matasa aiki a babban birnin kasar domin magance matsalar rashin aikin yi a tsakanin matasan Kongo.

“Tsarinmu shi ne mu tabbatar kowa na da aikin yi a babban birnin Kongo zuwa 2030,” in ji Tysia.

Fiye da kasuwanci

Babban burin La Kinoise shi ne ya mamaye kasuwar gahawa ta duniya, lamarin da wadda ta kirkiro kamfanin Tysia take ganin zai yiwu duk da ana jibge sauran kamfanonin gahawa a shaguna daga kasashe na fadin duniya.

“Domin farawa, muna so mu samar da wata al’ada a Jamhuriyyar Dimokradiyyar Kongo ta mutane su rinka shan kofin gahawa kafin su je wurin aiki, kamar a China inda suke da shayinsu na al’ada,” in ji Tysia.

“Yadda ‘yan China ke ba shayi muhimmanci yana kayatar da ni. Idan muka ba shayin Kongo irin wannan muhimmancin, ina ganin za mu mamaye duka Afirka da duniya.”

Tuni matashiyar ta ci kyaututtuka da dama. Daga ciki har da kyautar da ta samu ta “Strong Lady” da kuma “Woman of Merit” wadanda duka kyaututtuka ne na karfafa gwiwa ga mata.

Haka kuma tana cikin mata 100 wadanda suka fi fada a ji a Afirka, wadanda jaridar Forbes suka zaba.

“Babban burin kamfanin shi ne ya mayar da kasar Congo sanannar kasa ta hanyar gahawa,” in ji Tysia.

Gomman amalanke na kamfanin ke shawagi a duk safiya kan titunan Kinshasa domin jama’a su samu gahawa mai kyau a farashi mai rahusa ga kowa.

“Muna raba gahawarmu a gidajen abinci da manyan shaguna da ote-otel da sauran wurare da mutane za su iya sayen abinci,” kamar yadda ta bayyana.

DRC na ta kokari domin ganin ta zama daya daga cikin kasashen duniya masu samar da gahawa. Hoto/La Kinoise

Da alama mazauna Kinshasa sun soma zuwa wurin sayar da da gawahar.

“Tun lokacin da na gano ana sayar da gahawa kan titunan Kinshasa, ina tashi da safe, na shiga motata na siya gahawa a kan hanya, na je opis na sha kofin gahawana,” in ji Jean Nyembo.

Yana fatan ya ga ranar da La Kinoise za su kai masa gawaha har gida.

Tsohuwar al’adar gahawa

Jamhuriyyar Dimokradiyyar Kongo na da kasar noma mai girma. Kusan 1980, kasar Zaire a baya (DRC) na fitar da gahawa zuwa Amurka da Sudan da Habasha.

A baya tana samar da tan 500,000 a duk shekara, idan aka kwatanta da tan 10,000 da take samarwa a halin yanzu.

Tsawon shekaru, gwamnatin Kongo tana kula da fitar da kayayyaki, wanda hakan ke kawo cikas ga kamfanoni masu zaman kansu kamar su La Kinoise.

Kalubalen suna da yawa, da suka hada da yawan dauke wuta, lamarin da ke tilasta kasuwanci da dama su koma amfani da janareto, inda karin kudin mai kan kasuwancin ke kara kudin da suke kashewa da dubban daloli.

Haraji iri daban-daban da kuma matsalolin da suka shafi sufuri suna daga cikin matsaloli a yankin inda suke kara sa abubuwa su yi wahala.

“La Kinoise bai zama saniyar ware a wadannan matsalolin ba. Hanyoyi ba su da kyau, wanda ke haddasa matsalolin kai kayayyaki a cikin biranen DRC.

Wani lokacin idan ta kama dole, dole ne a tura kayayyaki ta jirgin sama, kuma hakan yana jawo kashe kudi sosai,” kamar yadda Tysia ta bayyana.

Masu sayar da gawaha na son tallafi

Roger Tata, wanda darakta ne a Kawa Kanzururu Cooperative da ke Jamhuriyyar Dimokradiyyar Kongo, wanda kamfani ne da ke noman gahawa a gabashn Kongo, ya tuna da cewa Zaire a baya tana daga cikin kasashen duniya da ke fitar da gahawa kafin yaki ya yi wa kasar illa a 1996.

La Kinoise na daga cikin kamfanoni masu zaman kansu da ke son farfado da shan gahawa a DRC. Hoto/La Kinoise

An samu raguwa a samar da shi bayan nan, lamarin da ya tilasta wa manoma barin gonakinsu sakamakon rashin tsaro.

“Mun ga tafiyar masu zuba jari da dama wadanda suka zuba jari kan gahawa da kuma yadda aka bar gonaki, wanda ya jawo matukar koma baya ga gahawan Kongo a kasuwar duniya. Muna kan hanyar sake farfadowa,” in ji Tata.

“Akwai bukatar kamfanoni su dawo, amma suna bukatar tallafin gwamnatin Kongo.” Baya ga inganta tsaro a wuraren da ake shuka gahawa, masu shuka gawahar suna son a daina biyan wasu haraji.

“Muna so a janye batun biza ga ‘yan kasuwa masu son siyan gahawa. Kasarmu ta samar da tan 120,000 na gahawa a duk shekara kafin 1980, kuma a yau muna samar da tan 11,000.

“Babbar raguwa ce wannan,” kamar yadda Tata ta bayyana.

TRT Afrika