Mambobin kungiyar Jeunes Volontaires pour l'Environnement (JVE-Bénin) sun sauya tattakin motsa jiki ana tsince shara "Eco-jogging" zuwa wata kungiyar tsaftace muhallin garuruwa da biranen Benin. Photo: Abdou Latif Adéyemi Oloude

Ba za ka yi tsammanin wani zai saka buhunhuna, da safar hannu ta leda, da cebur da kuma tsintsiya a cikin jakar tafiya tattakin motsa jiki na safiya ba.

Amma Abdou Latif Adéyemi Oloude ba mai tattakin motsa jiki da aka saba ganin irinsa ba ne, wanda ke nisan zango da ƙona kitse da kuma tura hotunan wuraren da yake ratsawa yayin motsa jiki, a kafar intanet ta Strava.

Wannan matashin ɗan fafutikar ɗan ƙasar Benin, a zahiri , mai cika-aiki ne na muhalli, yayin da yake bi yana kwashe shara da ledoji a matsayin wani ɓangare na tattakin motsa jikin da ya saba yi.

Oloude ɗaya ne daga cikin mutane da yawa. Mambobin kungiyar Jeunes Volontaires pour l'Environnement (JVE-Bénin) sun zamar da "Eco-jogging" wata kungiyar tsaftace garuruwa da biranen wannan ƙasa ta Yammacin Afirka.

Eco-jogging, kamar yadda sunan ya nuna, wani shiri ne da ya ƙunshi gaurayen motsa jiki da kuma kula da muhalli.

Mahalarta suna tattakin motsa jiki yayin da kuma suke tsince shara, musamman ledoji.

Da zarar an kammala tsaftace wuri, sai su koma na gaba, haka za a yi ta yi. Oloude ya fara harkar tasa ce a kudancin Abomey Calavi ta Benin, kuma tun wannan lokacin labari ya karaɗe wasu sassan ƙasar.

"Mu ƴan sa-kai ne da muke gudanar da ayyuka a ƙasashe da dama. Hadafin shi ne bayar da gudummawa wajen kare muhallin da ake rayuwa a cikinsa da kuma samar da abin yi ga matasa, mata da kuma waɗanda ba a damawa da su ta hanyar bayar da ilimi da koyar da dabarun zaman duniya,"a cewar Oloude.

Abokanan karatun Abdou Latif Adéyemi Oloude a cikin makaranta sun laƙaba masa inkiyar SuperEco saboda shauƙin kula da muhalli da yake da shi./Photos: Abdou Latif Adéyemi Oloude

Bin abu a sannu,an gina shirin Eco-jogging ne kan tunanin cewa duk wani al'amari na haɗin gwiwa da ya ƙunshi muradun bai-ɗaya kuma hanyar cim ma masa ta kunshi nishaɗi wannan burin ba makawa zai iya cika.

Ƙaunar tattakin motsa jiki da son tsaftace muhalli da suke da shi, shi ya haɗa ƴaƴan kungiyar sa-kai ta JVE-Bénin wuri guda.

"Galibi muna farawa da haɗuwa waje ɗaya dukkanmu ne, sai mu ɗan jijjiga jiki kamar yadda aka saba.

Daga nan sai mu gabatar da hanyoyin da za a bi a wannan ranar," Oloude ya sheda wa TRT Afrika.

"Domin samar da yanayi mai walwala, wataƙila a samu ƴan kaɗe-kaɗe da bushe-bushe, abin da shi ma kan taimaka wajen jawo hankalin masu wucewa. Duk wanda ya riske mu cikin aikin a bayyane yake yana da sha'awar abin da muke yi."

Oloude na kallon karfafa guiwa da kuma taya su da mutane a kan titi da sauran wuraren taruwar jama'a ke yi a matsayin wata manuniya ta yiwuwar shirin na Eco-jogging zai bunƙasa fiye da yadda ya zata tun da farko da ya soma.

Kama daga wuraren da aka yi shuke shuke a Jami'ar d'Abomey-Calavi, da Place de l'Amazone, ko Place des Martyrs a Cotonou, akwai tabbacin cewa, tawagar mutum 100 mai ƙarfin gaske ta JVE-Bénin eco-jogging, za ta iya nuna ƙwazonta.

Tawagar Eco-jogging ta Benin na jan hankalin sauran mutane wajen aikin tsaftace muhallin./Photo: Abdou Latif Adéyemi Oloude

Oloude ya yi nuni da cewa sharar ledoji sune kan gaba wajen jawo ƙazanta a galibin birane.

Matsalar zubar da shara

Wata muƙalar Bankin Duniya kan samarwa da sarrafa sharar ledoji ta ruwaito cewa a shekarar 2018 kawai, an zubar da ton miliyan 6.9 na sharar ledoji a ƙasashen Yammacin Afrika 17 da ke gaɓar teku.

Duk da Benin ta haramta amfani da leda a shekarar 2017 don bunƙasa amfani da kayan da ake ƙara sarrafawa, amma alƙaluma dake ƙasa sun nuna saɓanin hakan.

A cewar alƙaluma bayanai game da leda a Benin, a 2019, alal misali, an shigo cikin ƙasar da leda mai nauyin kg miliyan 6.7, da suka haɗa da nau'o'in polyvinyl, ethylene, da aluminium, dukkansu marasa ruɓewa.

Idan aka yi la'akari da wannan, wanda shi ne karɓaɓɓen ma'auni a faɗin nahiyar, Oloude ya tattaro matasa,galibinsu ɗalibai,su tunkari matsalar muhallin ƙasarsa.

"Ina ɗan shekaru 20 da haihuwa lokacin da soyayyar da nake yi wa halittu ta kai ni sashen sauyin yanayi da muhallin da halittu ke rayuwa na cibiyar Institut du Cadre de vie a Jami'ar Abomey-Calavi," inji matashin ɗan rajin kare muhallin da ake yi wa laƙabi da"SuperEco".

"Abin da muke buƙata daga hukumomi shi ne goyon baya. Muna so su mu'amalanci kungiyoyi dabam dabam da ke fafutika kan wannan lamari. Za mu so mu ga cewa dalibai da ma kowa da kowa a al'umma sun bayar da gudummawa gwargwadon karfinsu wajen kare muhalli."

Eco-jogging na tsaftace Benin, titi da tituna,da garuruwa da birane/ Photo: Abdou Latif Adéyemi Oloude

A watan Yulin shekarar 2023, Salvator Niyonzima, zaunannan jami'in tsare-tsare na Majalisar Ɗinkin Duniya a Benin, ya yi zargin cewa yin amfani da kaya dangin leda sau ɗaya su tashi a aiki shi ne babban dalilin yawaitar sharar da ba ta ruɓewa a ƙasar.

Yayin wani gangamin tsaftace muhalli, an kwashe sharar ledoji mai nauyin kilogiram 2,150 a cikin sa'a guda a gundumar Zango da ke Cotonou.

Oloude ya yi imanin cewa matsalar sharar ledoji za ta ƙara ta'azzara ne kawai idan ba a samu masalaha mai ɗorewa mai nasaba da gagarumin wayar da kan jama'a ba.

"Kare muhallin abin da ya shafi kowa ne, ba wai abin da ya shafi ƙwararru a fagen ba ne kaɗai," ya faɗa wa TRT Afrika.

TRT Afrika