Har yanzu Bakaken fata 'yan Afirka ta Kudu wadanda su ne suka fi yawa suna baya a wajen damarmaki na samun aiki.  / Hoto: Getty Images

Jam'iyyar African National Congress ANC wadda ta shafe shekaru 30 tana mulki ba tare da kalubalantarta ba har sai da ta rasa rinjayen a majalisar dokokin kasar a zaben watan Mayu, tana fuskantar matsin lamba kan ta inganta rayuwar Bakar fata da aka bar su a baya sakamakon mulkin 'yan tsiraru na shekaru da dama.

Jam'iyyar ANC wadda ta shafe shekaru 30 tana mulki ba tare da kalubalantarta ba har sai da ta rasa rinjayen a majalisar dokokin kasar a zaben watan Mayu, tana fuskantar matsin lamba kan ta inganta rayuwar Bakar fata da aka bar su a baya sakamakon mulkin 'yan tsiraru na shekaru da dama.

Dokar ta bunƙasa baƙaƙen fata da aka kafa a 2003 ta ƙirƙiri tsarin ba da maki wanda ke ƙarfafa kamfanoni su ɗauki baƙar fata aiki su kuma ringa ƙara musu girma, yayin da su kuma za su ringa samun sassaucin haraji da kuma damar samun kwangilar gwamnati.

Bayan shekaru 20, rashin aikin yi na bakaken fata ya ninka har sau biyar fiye da na farar fata, kuma rashin daidaito wajen samun kudin shiga shi ne mafi muni a duniya, a cewar Bankin Duniya, kuma masu suka sun ce manufar karfafawar ba ta yi aiki yadda ya kamata ba.

Reuters