Wasu daga cikin kadarorin da Masar za ta sayar suna bangaren albarkatun mai da sinadarai. Hoto: Reuters

Masar ta rattaba hannu kan kwangilolin sayar da hannayen jarin kadarorin gwamnati da darajarsu ta kai dalar Amurka biliyan 1.9, a wani bangare na shirin bunkasa kamfanoni masu zaman kansu da kuma tara kudaden kasashen waje da ke karancin samu, a cewar Firaiministan kasar Mostafa Madbouly a ranar Talata.

Ana ganin wannan yunkuri na sayar da kadarorin a matsayin wani mataki da ke da matukar muhimmanci ga Masar wajen ba ta damar rage tsawaita matsin lamba da take samu kan kudin fam na kasar, tare da janyo hanyoyin samun dalolin kudi da kaddamar da sauye-sauyen tattalin arziki karkashin shirin Asusun ba da Lamuni na Duniya IMF na dala biliyan uku.

Daga cikin dala biliyan 1.9 da kasar za ta samu, za a biya dala biliyan 1.65 da kudaden waje, in ji Madbouly.

Gwamnatin dai, ta kuduri aniyar tara dala biliyan biyu daga sayar da hannayen jarin kasar a karshen watan Yuni, sai dai ta fuskanci tsaiko sakamokon faduwar darajar kudin fam a kasuwar bayan fage.

Kudin fam na Masar ya yi asarar darajarsa da kusan rabin a kan dala tun watannin farkon shekarar da ta gabata, inda aka samu hauhawar farashin canji a hukumance da kuma farashin kayayyaki.

Sabbin kwangilolin sun hada da yarjejeniyar sayar da wasu tsirarun hannayen jari a wasu kamfanonin albarkatun mai uku ga asusun dukiya na Hadaddiyar Daular Larabawa ADQ a kan dala miliyan 800, a wata yarjejeniyar tara dala miliyan 700 don zuba jari a otel-otel na kasar da kuma yarjejeniyar kashi 31 cikin 100 na hannayen jari a kamfanin karafa na Ezz Dekheila wanda ya kai dalar Amurka miliyan 241, a cewar ministar tsare-tsare Hala el-Said.

"Duk an yi wadannan kuma an aiwatarsu," in ji Said, bayan wani taron manema labarai da ta samu halartar manyan jami'an majalisar ministocin kasar.

Hannayen jarin da aka siyar na otel-otel din, sun hada da kadarorin tarihi da ke Alkahira da Alexandria da Luxor, an bayar da su ne ga ICON, a cewar Talaat Mostafa ta bangaren karbar baki na kungiyar gine-gine da tsare-tsaren Masar.

Gwamnati ta kusan rabin kwatan jerin sunayen kamfanonin kasar 32 da ta sanar cewa za ta sayar da hannayen jari cikinsu, kuma tana shirin sayar da hannayen jari wasu kamfanoni a nan gaba, in ji Madbouly.

Ministan ya kara da cewar Masar na sa ran kara yawan kudin da ke shigowa kasar da dala biliyan 70 a kowace shekara domin ya kai dala biliyan 191 a shekarar 2026.

Wasu ma’amalolin cinikayya da gwamnati ke sa ran kammalawa a cikin 'yan watanni masu zuwa sun hada da yarjejeniyar sayar da filin gona na Gabal El Zeit kan farashin kudi fiye da dala miliyan 300 da kuma sayar da man fetur na Wataniya, mallakin sojoji da wata tashar wutar lantarki da Siemens ta gina, a cewar Said a yayin zantawarsa da manema labarai.

TRT Afrika