"Yan majalisar dokokin Amurka na sanya idanu kan dangantakar Afirka ta Kudu da Rasha. Hoto: AA

Afirka ta Kudu za ta karbi bakuncin kasashen duniya a taron bunkasa kasuwanci a watan Nuwamba, duk da kiran da wasu 'yan majalisar dokokin Amurka suka yi na hana kasar gudanar da taron saboda alakarta da Rasha, da kuma yadda ta bayar da dama ga jirgin ruwan Rasha ya tsaya a kusa da Cape Town a bara.

'Yan majalaisar sun yi wannan kira ne karkashin dokar AGOA - wata dokar Amurka da ta bai wa kasashen Afirka damar sayen kayayaki daga kasar ba tare da biyan haraji ba matukar sun cimma wasu sharudda, da suka hada da "dole su janye duk wani shinge da ke hana Amurka kasuwanci da zuba jari a kasashensu, su kuma samar da tsare-tsare na rage talauci, yaki da cin hanci da rashawa, da kare hakkokin dan adam."

A farkon wannan shekara, wasu mambobin majalisar dokokin Amurka daga jam'iyyun Democrat da Republican suka yi kira ga Sakataren Harkokin Waje Antony Blinken da dauke taron zuwa wani waje na daban, saboda zargin Afirka ta Kudu da bayar da makamai ga Rasha a yakin da take yi a Yukren.

Taimaka wa Rasha

Sun bayyana cewa mayar da taron zuwa wata kasa zai aike da sakon cewa Amurka ba za ta lamunci ganin abokan kasuwancinta na taimaka wa mamayar da Rasha ke yi a Yukren ba, sannan hakan zai tuhumi ko Afirka ta Kudu na da 'yancin amfana daga AGOA.

Sun kuma bayyana yadda Afirka ta Kudu ta karbin bakuncin Rasha da Amurka wajen hakar mai a farkon wannan shekarar. An kuma soki Afirka ta Kudu kan yadda ta ki fitowa karara ta soki Rasha sakamakon mamayar Yukren.

Amurka da Afirka ta Kudu sun fitar da sanarwar hadin gwiwa da ke cewa za a gudanar da taron a birnin Johannesburg, wanda hakan ke nufin an daidaita bayan watannin da aka dauka ana rikicin diplomasiyya.

"Ina sauraron na ziyarci Afirka ta Kudu a watan Nuwamba, don tattauna wa kan abubuwan da muka baiwa fifiko, sake tabbatar da kokarin gwamnati ga nahiyar, da tattauna damarmakin da za su karfafa ayyuka AGOA a yayin da muke zurfafa kasuwancinmu da kasashen Afirka," in ji Wakiliyar Kasuwanci ta Amurka Katherine Tai.

Manyan masu amfana

Afirka ta Kudu na daya daga cikin mafiya amfana da AGOA, inda kayan da take fitar da kayayyakinta zuwa Amurka ya kai na dala biliyan uku a 2022.

Kakakin Ma'aikatar Harkokin Wajen Afirka ta Kudu, Clayson Monyela ta yaba da sanarwar, inda ta bayyana ta a matsayin "nasara ga diflomasiyyar Afirka ta Kudu."

"Wasu sun roki da a mayar da taron daga Afirka ta Kudu, kuma ma a kori kasar daga amfana da AGOA. Wasu ma sun ce za a hukunta kasar da takunkumai. Diflomasiyya da dabarun ayyukanmu sun yi nasara," in ji Monyela a wata sanarwa ta shafin Twitter.

Makamai ga Rasha

Kwamitin da Shugaban Kasar Afirka ta Kudu Cyril Ramaphosa ya kafa don binciken zargin Afirka ta Kudu ta loda makamai a jirgin ruwan da zai tafi Rasha ya bayyana babu shaidar hakan, wanda kuma an sanar da jakadan Amurka a Afirka Reuben Brigety wannan cigaba.

Kwamitin ya kuma gano Afirka ta Kudu ba ta san cewa jirgin ruwa da ke dakon makaman Rundunar Sojin Kasar daga Hadaddiyar Daular Larabawa jirgi ne na Rasha da Amurka ta saka wa takunkumi.

Shugabanni daga kasashen Afirka da dama da kungiyoyi masu zaman kansu za su halarci taron a tsakanin 2 da 4 ga Nuwamban bana.

TRT Afrika