Shugaban Jamhuriyar Nijar Mohamed Bazoum ya karbi bakuncin ministocin sufuri da kasuwanci daga Jamhuriyar Benin da Burkina Faso da Togo da kuma na kasarsa don su yi masa karin haske kan abin da suka tattauna a taronsu kan kasuwanci maras shinge.
Wata sanarwa da Fadar Shugaban Nijar ta wallafa a shafinta na sada zumunta ranar Alhamis ta ambato Ministar Masana'antu da Kasuwanci ta Benin Mrs Assouman Alimatou Shadiya tana cewa Ministocin sun gana ne kan yadda za a samar da yanayi mai kyau na yin kasuwanci maras shinge a tsakanin kasashen.
Ta ci gaba da cewa kasashen Nijar da Burkina Faso, wadanda ba su da teku, suna da damar amfani da tashar jiragen ruwa ta Cotonou da kuma ta Lomè don cimma burinsu.
Ta ce ba sabon abu ba ne kasashen hudu su hada hannu wajen tafiyar da tashoshin.
"Wannan ya sa muke ganin akwai bukatar sake nazari kan tsare-tsaren sufurin kaya da jama'a don taimakawa wajen ci-gaban wadannan kasashe makwabta kuma 'yan uwan juna," in ji Mrs Assouman Alimatou Shadiya.
"Mun samu kwarin gwiwa daga Shugaban Nijar Mohamed Bazoum, hakazalika shugabannin kasashen Benin da Togo da Burkina Faso su ma sun ce za su taimakawa wajen kasuwanci don hakan ya zama hanyar samun kudin shiga da samar da ginshikin ci gaba ga kasashenmu," in ji ta.
Masana tattalin arziki sun ce wadannan kasashe suna da babbar damar hada kai domin inganta rayuwar al'ummarsu ta hanyar kasuwanci, ganin cewa suna cikin mafi fama da talauci a duniya.