COMESA sun gudanar da taronsu na bana a Lusaka babban birnin Zambia. / Hoto: AFP

Shugaban Kasar Kenya Willia Ruto ya yi kira da a samar da kudin bai daya na Afirka domin saukaka kasuwanci tsakanin kasashen nahiyar.

A yayin da yake gabatar da bayaninsa a wajen Taron Kasuwar Bai Daya ta Gabashi da Kudancin Afirka (COMESA) a Lusaka babban birnin Zambia, Ruto ya bayyana cewa tabbatar da hadin kan kasuwancin yankuna na nufin jama’a ba za su damu kan da wanne kudi za su yi cinikayya ba.

Ruto ya ce ”Jama’armu ba sa iya cinikayya ba tare da damuwa kan wanne kudi ne za su yi amfani da shi ba. Wannan da ma wasu matsaloli da ba na kudi ba, na daga abubuwan da ya zama dole a magance cikin gaggawa don jama’armu su samu damar gudanar da kasuwanci da hade wa waje guda.”

An gudanar da taron mai taken “Hadin kan tattalin arziki don bunkasar COMESA bisa tubalin zuba jari, habaka kudade da yawon bude ido.”

A nasa jawabin, shugaban kasar Malawi Lazarus Chakwera ya bayyana cewa yankin ba zai sake asarar lokaci ba wajen ganin an cimma burin hadewa waje guda.

Chakewar ya ce “Damar mu’amalar kasuwanci a tsakanin mambobin COMESA abu ne mai girman gaske, dole a ci gaba da bunkasar da habakar kudade da samar da kayayyaki, hakan na nufin ba za mu yi sakacin zama a baya ba a bukatar neman hade yankunanmu waje guda,”

Shugaban COMESA kuma shugaban kasar Masar Abdulfatah Al-Sisi ya ce yankin mai mutane miliyan 720 na da kasuwancin dala miliyan 580, babu dalilin da zai hana a habaka kasuwanci a tsakanin kasashensa.

Al-Sisi ya yi kira ga kasashen COMES da su hada hannu waje guda don gina kayan more rayuwa da za su saukaka kaiwa da komowar kayayyaki da mutane a yankin don habaka hadewa waje guda.

Mai masaukin baki kuma shugaban kasar Zambia Hakainde Hichilema ya bayyana cewa dole yankin ya tabbatar da samuwar zaman lafiya, tsaro da kwanciyar hankali saboda su ne ginshikan cigaban zamantakewa da tattalin arziki.

Al -Sisi ya mika shugabancin COMESA ga Hichilema a karshen taron.

AA