Aan sa rai wannan aiki zai samar wa miliyoyin mutane ayyukan yi. Hoto/OTHER

Gwamnatin kasar Kamaru za ta soma gina layin dogo a watan Agusta domin hada yankin tekunta da wurin da ake da tarin ma'adanai na tama da ke kan iyaka da Jamhuriyar Dimokuradiyyar Kongo.

Kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ambato ministan tama da karafa na kasar yana bayyana haka a ranar Talata.

Aikin gina layin dogon da zai hada wurin hakar ma'adanai na Nabeba zuwa garin Kribi mai tashar jiragen ruwa da ke kudancin kasar zai soma ne a karshen watan Agusta a garin Ntam, a cewar Minista Fuh Calistus Gentry bayan ya gana da jami'an ma'aikatar ma'adanai ta Jamhuriyar Dimokuradiyyar Kongo.

"Dukkanmu za mu iya nuna wa duniya cewa muna da azamar da za mu tabbatar da ganin al'ummomin da ke zaune a yankuna masu ma'adanai na Kamaru da Kongo suna iya zama tare," in ji shi.

Ministan ya kara da cewa sun gano sabbin wuraren hakar ma'adanai 12 a Kamaru, yana mai cewa za a soma aiki a biyar daga cikinsu a wannan shekarar. Bai yi karin bayani kan hakan ba.

A 2021 Kamaru ta sanya hannu kan yarjejeniya da wakilan kamfann Aust-Sino Resources and Bestway Finance don gina layin dogo mai nisan kilomita 500, wanda zai iya daukar tama mai nauyin tan miliyan 35 a duk shekara tsawon shekaru goma.

Kamfanin Bestway Finance an yi masa rajista a Hong Kong. Shi kuma kamfanin hakar ma'adanai na Aust-Sino yana da mazauni a Australia, amma wasu daga cikin manyan jami'ansa suna da alaka da China, a cewar shafin intanet na kamfanin.

Reuters