Kamfanin Meta mallakin Facebook da Instagram ya ce zai shimfida wata wayar kebul a karkashin teku da za ta ratsa zuwa nahiyoyi biyar domin daukar bayanai, gami da bunkasa fasahar ƙirƙirarriyar basira.
Za a shimfiɗa kebul ɗin a tsawon fiye da kilomita 50,000 (mil 31,000) tsakanin Amurka da Afirka ta Kudu da Indiya da Brazil da "sauran yankuna", kamar yadda Meta ya wallafa a wani shafi a ranar Juma'a.
Sadarwar dijital ta duniya ta dogara ne da babbar hanyar sadarwa ta ƙarƙashin ruwa, wanda aka riga aka girka kebul mai tsawon kusan kilomita miliyan 1.2, a cewar wani rahoto na 2024 na Cibiyar Dabaru da Nazarin Ƙasashen Duniya (CSIS na Amurka).
Manyan kamfanonin dijital kamar Meta a kwanan nan suna saka ƙarfi a harkar dasa kabul a cikin teku, wanda a baya kamfanoni kamar SubCom na Amurka, ASN na Faransa, NEC na Japan da HMN na China ne suka mamaye harkar.
Yawan lalacewa
Ana amfani da hada-hadar tattalin arziki ta ƙarƙashin teku wajen watsa bayanai ga ƙasa da ƙasa, amma suna yawan lalacewa akai-akai daga abubuwan da suka faru kamar zaizayar ƙasa a ƙarƙashin ruwa ko tsunami da sauran su.
Hakanan za su iya zama abin kai hari da gangan ko don zagon ƙasa da leƙen asiri.
A watan Janairu ne kungiyar tsaro ta NATO ta kaddamar da sintiri a Tekun Baltic bayan da ake zargin an kai hari kan wayoyin sadarwa da igiyoyin wutar lantarki da masana da 'yan siyasa suka ɗora laifin a kan Rasha.
Shirin na Meta wanda aka yiwa laɓabi da "Project Waterworth", yana nufin "ƙarfafa ma'auni da amincin manyan hanyoyin dijital na duniya ... tare da wadatar gagarumin haɗin gwiwa da ake buƙata don haɓakar AI".
Kamfanin ya ce aikin na kebul din USB zai ci "biliyoyin daloli da zuba jari na shekaru da yawa".
Buga misali da AI da Meta ta yi a matsayin dalilin sanya kebul ɗin yana ba da haske game da ƙarancin cigaban fasaha na bayanai, wanda mai yuwuwa zai haɓaka ayyukan dijital na duniya har abada a cikin shekaru masu zuwa.