Sashen kasuwanci na kamfanin Facebook 'Meta Business' ya ce gwamnatin Ghana ta umarce shi ya soma karbar harajin kashi 21 kan tallace-tallacen da ake yi a manhajar a cikin kasar.
Meta ya bayyana haka ne a wata sanarwa da ya fitar ranar Alhamis.
Ya ce zai soma karbar harajin daga ranar 1 ga watan Agusta mai zuwa.
"Gwamnatin Ghana ta umarci Meta ya karbi haraji daga masu son yin talla - na kashin kansu ko na kasuwanci", kamar yadda wani sakon imel na Meta Business ya bayyana.
“Idan ka yi rajista ta biyan haraji na VAT ka bayar da sunanka da adireshinka da kuma shaidar katinka na haraji, duk wadannan bayanan za su nuna cewa ka yi talla kamar yadda ya dace," in ji sanarwar.
Masana harkokin kasuwanci sun ce wannan matakin zai taimaka wa Ghana bunkasa hanyoyin samun kudin shigarta.