Ana samar da koko a kasashe irinsu Ivory Coast da ke Yammacin Afirka sannan a kai shi kasashen Turai don sarrafa shi wurin yin cakulet./Hoto:  REUTERS/Luc Gnago

Farashin koko ya yi tashin da bai taba yin irinsa ba a cikin shekara 46 a kasuwar cinikinsa da ke birnin Landan ranar Laraba.

Hakan na faruwa ne a yayin da mummunan yanayi a Yammacin Afirka yake barazana ga noman koko don kai shi kasashen da ke sarrafa shi wurin yin cakulet.

An sayar da kowanne metirik tan na koko a kan fam 2,590 ranar ta Laraba. Wannan ne karon farko da aka sayar da shi a irin wannan farashi tun 1977, shekarar da aka yi cinikin kowanne metirik tan na koko a kan fam 2,594.

Farashin koko na tashi ne sakamakon karancinsa a kasuwar hada-hadar koko ta duniya idan kasashen da ke noma shi - Ivory Coast da Ghana suka fuskanci matsala.

Bayanai sun nuna cewa an samu raguwar fitar da koko daga Ivory Coast da kashi 5 cikin dari a kakar bana.

A wannan watan hukumar da ke cinikin koko ta duniya (ICCO) ta ce za a fuskanci gibin samar da koko a fadin duniya inda zai ragu daga metirik tan 142,00 zuwa 60,000.

"Wannan ce kakar koko ta biyu a jere da ake fuskantar gibin samar da shi," a cewar Leonardo Rosseti, wani mai sharhi kan kasuwar koko ta StoneX.

Ambaliyar ruwan da ake fama da ita a wasu gonakin koko na kasar Ivory Coast na cikin abubuwan da ke haddasa karancinsa.

Reuters