An raba jimillar Naira Tiriliyan 1.703 na Harajin Asusun Tarayya na watan Janairun 2025, ga Gwamnatin Tarayya da Jihohi da Kananan Hukumomi.
Wannan na ƙunshe ne a wata sanarwa da Daraktan Yada Labarai da Hulda da Jama’a na Ofishin Akanta Janar na Tarayya, Bawa Mokwa ya fitar a ranar Alhamis.
Mokwa ya ce an raba kudaden shigar ne a taron kwamitin raba kudaɗen haraji na tarayya a ranar Alhamis a Abuja.
A halin da ake ciki kuma, sanarwar da aka fitar bayan taron na FAAC ta bayyana cewa, jimillar kudaden shigar da suka kai tiriliyan ₦1.703 sun ƙunshi waɗanda doka ta tanada na ₦749.727, da kuma karin harajin da ya kai biliyan ₦718.781.
Har ila yau, ya ƙunshi harajin da ake cire wa inda an tura kuɗi ta banki wanda ya kai snaira biliyan 20.548.
Sanarwar ta kuma nuna cewa an samu jimillar kudaden shigar da ya kai tiriliyan 2.641 a watan Janairun 2025.
Ta ce jimillar kudaden da aka kashe na kudin da aka tara ya kai Naira biliyan 107.786 yayin da jimillar kudaden da aka kashe, da yin aiki da kuma maido da su ya kai Naira biliyan 830.663.
Sanarwar ta ce daga cikin jimillar kudaden shigar da ake rabawa na Naira Tiriliyan 1.703, Gwamnatin Tarayya ta samu jimillar Naira Biliyan 552.591, yayin da gwamnatocin Jihohin kasar suka samu Naira Biliyan 590.614.
Sai ƙananan hukumomi da suka samu naira biliyan ₦434.567, kuma an raba jimillar jimillar biliyan ₦125.284 (kashi 13 na kudaden shiga na ma'adinai) ga jihohin da suke amfana a matsayin kudaden shiga.