Turkiyya da Sudan suna da alaƙa mai tarihi tun daga zamanin Daular Usmaniyya. / Hoto: AA

Ministar Harkokin Zuba Jari da Raya Kasa ta Sudan Ahlam Madani Mahdi Sabri ta bayyana cewa, masu zuba jari na Turkiyya na kara nuna sha'awarsu a Sudan, tana mai hasashen ƙaruwar zuba jari, musamman bayan taron tattalin arziki da ya haɗa shugabannin 'yan kasuwa daga kasashen biyu.

Ta bayyana hakan ne a wata tattaunawa da ta yi da kamfanin dillancin labarai na Anadolu a gefen taron kasuwanci na Turkiyya da Afirka karo na 12, wanda aka yi a Istanbul a ranar 12 ga watan Fabrairu na tsawon kwanaki biyu, wanda kuma ya karbi bakuncin taron kasuwanci tsakanin Turkiyya da Sudan.

Alaƙa mai tarihi

Turkiyya da Sudan suna da alaka mai tarihi kuma mai karfi tun daga zamanin Daular Usmaniyya, inda ake ci gaba da gudanar da manyan ayyuka a bangarori daban-daban, musamman a fannin siyasa da tattalin arziki.

Ta bayyana cewa, jarin da Turkiyya ke zubawa a Sudan ya riga ya taka muhimmiyar rawa, tare da yin mu'amalar kasuwanci tsakanin kasashen biyu, wanda ya kai kusan dalar Amurka miliyan 500, a cewar bayanan hukumomi.

Sabri ta bayyana cewa, a yayin tarukan tattalin arziki na baya-bayan da aka gudanar masu zuba jari na Turkiyya sun nuna sha'awarsu ta faɗaɗa kasuwancinsu a Sudan.

Ta kuma bayyana cewa, wata tawagar Turkiyya ta ziyarci kasar Sudan makonni biyu da suka gabata domin wani taron zuba jari, inda masu zuba jarin Turkiyya suka tabbatar da aniyarsu ta bayar da gudunmawarsu ga yunkurin sake gina kasar Sudan.

Dangane da muhimmancin taron tattalin arziki da aka gudanar a Istanbul, Sabri ta ce, "Wannan taron yana da matukar muhimmanci ga Sudan da ma kasashen Afirka baki daya, ganin irin rawar da Turkiyya ke takawa a fannoni da dama."

Ta kara da cewa, "Turkiyya kasa ce da ta ci gaba, kuma ta irin wadannan tarurrukan, ana kulla kawance mai karfi tsakanin kasashen Afirka da Turkiyya, tare da inganta hadin gwiwar tattalin arziki da kuma kara yawan ciniki."

TRT Afrika