Gwamnatin Ghana ta gano ma'aikatan bogi 80,000 a cikin tsarin biyan albashin ƙasar / Hoto: Reuters

Shugaban Ghana John Dramani Mahama a ranar Laraba ya ba da umarnin gudanar da bincike kan ayyukan hukumar da ke samar wa ɗaliban jami'an da aka yaye gurbin sanin makamar aiki tsohuwar gwamnatin ƙasar bayan gano wasu ma'aikatan bogi fiye da 81,000 da ake zargi akwai su a cikin jerin sunayen ma'aikata.

An gano sunayen ma'aikatan na bogi ne bayan aikin kidayar ma'aikata domin biyan basussukan kuɗaɗen alawus-alawus da ake biya a hukumar wadda ke kula da ayyukan da suka wajaba kan ma'aikata da suka kammala karatun digiri na shekara guda, kamar yadda sanarwar fadar shugaban ƙasar ta bayyana.

Ko da yake ba a san takamaiman ƙudaden da aka biya ma'aikatan ba ƙarkashin albashin na bogi.

Ma'aikatar kuɗi ta ƙasar ta fitar da cedi miliyan 226 na Ghana kwatankwacin dalar Amurka miliyan 14.6 a matsayin kuɗaɗen biyan albashin ma'aikata 98,000 da aka san da su, in ji sanarwar fadar shugaban kasar.

Ma'aikatar kudi ta fitar da cedi miliyan 226 na Ghana kwatankwacin dalar Amurka miliyan 14.6 a matsayin biyan kudaden da aka biya sama da 98,000 na halal, in ji sanarwar fadar shugaban kasar.

Yaki da cin hanci da rashawa

Shugaba Mahama, wanda ya dawo kan mulki a watan Janairu, ya yi alƙawarin kawar da matsalar cin hanci da rashawa a ƙasar wadda ke da arzikin man fetur da zinari a yankin Afirka ta Yamma wadda a yanzu take koƙarin farfadowa daga matsalar tattalin arziki mafi muni da ta taɓa shiga.

A ranar Labara, ofishin mai shigar da ƙara na musamman (OSP) a hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta Ghana, ya bayyana cewa ana neman tsohon minsitan kuɗin ƙasar Ken Ofori-Atta ruwa a jallo, bisa zarginsa da hannu a wasu hada-hadar kudaɗe guda biyar da ake bincike a kan su.

Reuters