Tinubu ya dakatar da dokar harajin ne don samar wa 'yan Nijeriya sauki, in ji sanarwar da ta fito daga fadar shugaban kasar: Hoto/twitter/fadan shugaban kasa

Shugaban Nijeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya ba da umarnin yin wasu sauye-sauye a harkar harajin kasar ciki har da dakatar da karbar harajin kashi 5% cikin 100 na layukan waya har zuwa watan Satumba.

Wata sanarwar da mai ba da shawara na musamman kan ayyuka na musamman da sadarwa ga shugaban kasar, Dele Alake, ya fitar, ta ce umarnin da shugaban ya bayar ya hada da dakatar da karbar haraji kan wasu abubuwan da ake kerawa a cikin kasar.

Sanarwar ta ce sai watan Satumba ne dokokin da tsohuwar gwamnati ta kafa za su fara aiki domin a bai wa masu masana'antu lokacin da za su shirya wa biyan harajin maimakon watan Mayun da ya gabata.

Alake ya ce yin hakan na nufin gwamnati ta bi sharadin ba da sanarwar kwana 90 kafin sauya dokar haraji kamar yadda tsarin haraji na kasa na shekarar 2017 ya tanada.

Kazalika, ya ce gwamnati ta dauki matakin nan ne bayan ta ji koke-koken ‘yan Nijeriya a kan haraji domin ta saukaka musu.

Ya jaddada cewar gwamantin kasar za ta sake duba korafe-korafen da ake yi kan karbar haraji da yawa da kuma matsalolin da ke takura wa kasuwanci.

Alake ya ce gwamnatin za ta ci gaba da samar da yanayin da zai sa kamfanoni su yi walwala.

TRT Afrika da abokan hulda