Ghana ta ci gaba da rike kambinta na kasar Afirka da ta fi kowacce fitar da zinare tare da kai shi kasuwannin duniya.
Wata sanarwa mai dauke da sa hannun Ministan Kasa da Albarkatun Kasa na Ghana Samuel A. Jinapor ta bayyana cewa, wannan nasarar ta samu ne sakamakon kyawawan ayyukan da gwamnatin Nana Akupo-Addo ke gudanarwa tare da hadin gwiwae Kungiyar “Yan Kasuwa da Masu Hakar Gwala-Gwalai ta kasar.
Zinaren da aka fitar a 2022 ya karu sosai sama da na shekarun baya
Adadin zinaren da aka fitar a 2022 ya kai yawan nauyin ounce miliyan 3.08 sama da nauyin ounce miliyan 2.72 da aka fitar a shekarar 2021.
Haka zalika fitar da zinaren zuwa kasashen waje da kananan ‘yan kasuwa ke yi ya karu daga ounce 98,001 a 2021 zuwa dubu 655,656 a 2022.
Jumullar zinariyar da aka fitar a Ghana a 2022 ya kama nauyin ounce miliyan 3.74, wanda a 2021 adadin yake miliyan 2.82.
Farfado da bangaren hakar zinare a Ghana ya taimaka
Sanarwar ta tunatar da yadda gwamnatin Ghana ta gyara ayyukan mahakar ma’adanan zinare a AgloAshanti Obuasi a 2016, wanda aka farfado da shi a 2019.
Sanarwar ta ce an kuma da wo da ayyukan hakar zinare a Bibiani a shekarar 2022, wanda aka dakatar shekaru bakwai da suka gabata.
Gyara wadannan cibiyoyin hakar ma’adanai tare da yadda gwamnati ta rage yawan harajin da take karba daga mahaka daga kaso 3 zuwa 15 cikin 100, sun sake karfafa gwiwar ma’aikatan hakar zinaren a Ghana.
Kaddamar da sabbin wuraren hakar zinare
A bayanin na Minista Jinapor ya yi bayanin kan yadda a nan wani lokaci za a kaddamar da sabbin wuraren hakar albarkatun zinare wanda hakan zai sake daga matsayin Ghana a wannan fanni.
Sanarwar ta ce “Nan da shekaru masu zuwa Ghana za ta habaka fiye da yadda ake zato. Tare da kaddamar da sabbin wuraren hakar zinare guda uku na; Cardinal Resurcec Namidini da ke Gabashin Ghana, Azumah Resources da ke Yammacin Ghana da Newmont Ahapo da ke arewacin kasar”.
Zinare na habaka tattalin arzikin Ghana
Zinare na ci gaba da zama ginshiki a cigaban tattalin arzikin Ghana.
Sanarwar ta bayyana yadda a shekarar da ta gabata Ghana ta samu dala biliyan 6.6 sakamakon fitar da albarkatun zinare zuwa kasashen waje.
Gwamnatin Ghana ta kudiri aniyar ci gaba da inganta harkokin hakar ma’adanan zinare ta hanyar karfafa gwiwar kananan masu hakar zinare a fadin kasar, musamman ma tare da kaddamar da manufar GoldI4.
Haka zalika gwamnatin ta yaba wa dukkan ma’aikatan hakar zinare bisa yadda suke bayar da hadin kai da goyon baya ga gwamnati.