Ma'aunin tattalin arzikin kasar ya karu da kashi 5.5 cikin 100 a wata ukun farko na 2023 idan aka cire albarkatun man fetur. / Photo: Getty Images

Hukumar kididdiga ta kasar Ghana, ta ce tattalin arzikin kasar ya karu da kashi 4.2 bisa ma'aunin GDP, a watannin farko na shekarar 2023 idan aka kwatanta da kashi 3.0 da aka samu a lokaci irin wannan a shekarar 2022 da ta shude.

Idan aka kwatanta da watannin baya na watan Oktoba zuwa Disamba na 2022, Ma’unin GDP na kasar ya karu da kashi 1.1 a watanin farko na 2023 da maki 0.3 bisa 100, sama da adadin da aka samu a rubu’i hudu na watanin cikin shekarar 2022.

A rahoton wata-wata da ake fitarwa kan ma’unin tattalin arzikin kayayyakin cikin gida na kasar, QGDP na watannin farko na shekarar 2023, sun hada da kiyasin farashin gas na watanni ukun farko na 2023 ya karu inda ya kai cedi biliyan 48.8 idan aka kwatanta da cedi biliyan 46.9 na watanni ukun farko na 2022.

Sannan kuma an samu kari a fannonin da ba na albarkatun man fetur ba a wata ukun farko na 2023 da cedi biliyan 46.5 idan aka kwatanta da cedi biliyan 44.1 na wata ukun farko na 2022.

Hakan na nufin ma'aunin tattalin arzikin kasar ya karu da kashi 5.5 cikin 100 a wata ukun farko na 2023 idan aka cire albarkatun man fetur.

TRT Afrika